Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Shugabannin hukumar shari’a da zakka a jihar Kano.
A yayin kaddamar da shugabanin hukumar ta shari’a, gwamna Yusuf ya nada sheikh Abbas Abubakar Daneji a matsayin Shugaban hukumar ta shari’a.
Gwamna Yusuf ya kuma nada mutane 16 da zasu jagoranci hukumar ta shari’a ciki harda shugabanta Sheikh Daneji.
Sauran Shugabannin hukumar shari’ar sun hada da Sheikh gwani Hadi Gwani Dahiru a matsayin kwamishina na daya da Sheikh Ali Dan Abba a matsayin kwamishina na biyu.
Sai Kuma Shiek Abubakar Mai Ashafa a matsayin Mamba,da Malam Naziru Saminu Dorayi shima Mamba da sauransu.
Yayinda kuma Dr Muhammad Sani Hashim zai kasance Sakataren hukumar ta Shari’a.
Rusau: Ana zargin an harbi mutane 6 a unguwar Rimin zakara dake Kano
A bangaren hukumar zakka da Hubusi,Kuma gwamna Yusuf ya nada Sheikh Barista Habibu Dan almajiri a matsayin Shugaban hukumar ta zakka.
Sauran mutanan sun hada da Sheikh Nafiu Umar Harazimi a matsayin Kwamishina na daya sai kuma Dr Ali Kurash a matsayin Kwamishina na biyu da sauransu.
A yayinda yake jawabi jim kadan da mikawa mutanan takardar kama aiki ,yace ya zabo sune a bisa cancanta da gogewarsu.
Ya horesu da su bada hadin kai wajen ciyar da Kano gaba.