Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Makaman Bichi Alhaji Isyaku Umar Tofa ya bukaci al’umma da suyi koyi da Dr. Muhammed Musa Zango wajan tallafawa al’umma da arzikin da Allah ya ba shi .
Alhaji isyaku Tofa ya bayyana hakan ne yayin taron da kungiyar hadinka cigaban unguwar Zango wato Zango community Development association ta Shirya domin karrama Dr. Muhammad Musa Zango .
Ya ce tabbas abubuwan alkhairin da Dr. Muhammad Zango yake yi abun a yaba ne kuma abun aikoyi da shi ne musamman bisa yadda yake tiritiri da al’umma wajan gina musu rayuwa .
“Babu shakka al’umma suna cikin mawuyacin hali akwai bukatar masu arziki su rika tallafawa masu karamin karfi, don fitar da su ko rage musu radadin halin da suke ciki”. Inji Alhaji Isyaku Umar
Ya kuma yabawa wannan kungiya bisa karramawar da ta yiwa Dr. Muhammad Zango, inda ya ce hakan zai kara masa kwarin gwiwar cigaba da tallafawa al’umma.
Musa Iliyasu ya bayyana dalilin da yasa Kwankwaso ke neman komawa APC yanzu
A nasa jawabin guda cikin wadanda suka shirya taron Hon. Shu’aibu Idiris Zango ya ce sun karrama Dr. Muhammad Musa Zango saboda irin gudunmawar da yake basu da sauran al’umma .
“Mu shirya masa wannan taron karramawar ne musamman saboda yadda shi a karankansa ya kafa Gidauniyar tallafawa al’umma a unguwar Zango wacce ake Kiran da FATAH ZANGO FONDATION Kuma ya asasata shi kadai ba tare da wani ba”.
Shu’aibu Idiris Zango ya godewa mahalarta taron, sannan ya yi kira ga sauran masu hannu da shuni da su rika tallafawa masu karamin karfi don saukaka musu.
APC ta kori tsohon ministan Buhari
Da yake nasa jawabin wanda aka shirya taron domin shi Dr. Muhammed Musa Zango ya nuna farin cikinsa bisa wannan karramawa da aka yi masa, sannan ya ce hakan zai kara masa kwarin gwiwar cigaba da tallafawa al’umma.
” Yanzu nan, Ina sanar da cewa duk masu fama da lalurar idanu su zo su karbi kati domin a duba su kuma a basu magani kyau nan take”. Inji Dr. Muhammad Musa Zango
Daga karshe ya kara dace wa ba zai taba gajiyawa ba wajen taimakan al’umma, inda kuma ya yabawa kungiyar bisa karramawar da ta yi masa, sannan ya basu tabbacin kofarsa a bude take domin cigaba da tallafawa al’umma.
Itama Anata bangaran uwar gidan Dr. Muhammed Musa Zango Barr. Hajiya Mardiyya Bashir salihi Magashi ta ce a shirye take ako da yaushe domin karfafawa mai gidanta gwiwa domin ya cigaba da rubanya aiyukan alkhairin da ya saba yi wa al’umma.
Taron dai ya gudana ne a Sani Abacha Stadium kofar Mata, taron ya samu halartar manyan Baki daban-daban daga ciki da wajan jihar Kano