Babban Daraktan kudi na hukumar raya kogunan Hadeja-Jama’are kuma jigo a jam’iyyar APC, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya yi zargin cewa Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran dariƙar Kwankwasiyya na yunkurin daidaitawa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya samu nasarar yin wa’adi na biyu na mulkin jihar a 2027.
Daily Trust ta rawaito cewa da ya ke zantawa da manema labarai a Kano a ranar Alhamis, Iliyasu, tsohon kwamishina ne a Kano , ya yi ikirarin cewa Kwankwaso na yunkurin komawa jam’iyyar APC ne domin buƙatar sa ta siyasa.
Ya kuma gargadi Tinubu da kada ya amince da Kwankwaso, domin “zai ci amanar sa a siyasa” kamar yadda ya yi wa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a baya.
Musa Iliyasu Kwankwaso dai ya jima yana adawar siyasa da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.