Daga Rukayya Abdullahi Maida
Mai baiwa gwamnan Kano shawara na musamman kan harkokin matasa da wasanni Sani Musa Danja ya ce ya shiga harkokin siyasa ne don ya ba da ta shi gudunmawa wajen inganta rayuwar al’umma ba don ya sami kudi ko mukami ba.
” Siyasa harka ce da zaka ba da taka gudunmawar don inganta rayuwar al’umma, sabanin yadda wasu suka dauke ta a matsayin wata harka da idan ya shigeta zai tara kudi don ya sami mukami”.
Sani Danja ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa ta musamman da yayi da wasu yan jaridu a Kano cikinsu har da jaridar Kadaura24.

Ya ce babban burinsa shi ne ya ga ya tallafawa rayuwar marasa karfi, saboda muddin mutum yana taimakon al’umma to za ka ga Allah ya shiga lamarinsa.
” Kokarin tallafawa rayuwar ya’yan talakawa da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso yake yi shi ne dalilin da yasa na ga dacewar na bi shi , saboda nima na bayar da tawa gudunmawar tunda manufarmu da shi Kwankwaso iri daya ce” . A cewar Sani Danja
Musa Iliyasu ya bayyana dalilin da yasa Kwankwaso ke neman komawa APC yanzu
Ya ce Bai taba damuwa don ba a bashi mukami ba, duk kuwa da dacewar da yayi ya na bin Kwankwaso sama da shekaru 20, ” burina yana cika saboda Ina baiwa wanda yake taimakon al’umma gudunmawa to na san nima Allah zai ba ni lada gwargwadon aikin da na yi”.
Sani Musa Danja ya kara da cewa “Wannan mukamin da gwamnan Kano ya ba ni ba wai na zo na sami kudi ba ne, a’a na zo ne don na yi aiki kuma na taimakawa masa mu inganta rayuwar matasan jihar Kano musamman wadanda suke abubuwan da basu dace ba”.
Masha warcin gwamnan kan harkokin matasa da wasanni ya ce yadda ya damu ya ga ya’yansa sun sami ingantaccen ilimin haka ya damu ya ga sauran matasan jihar Kano sun sami managarcin ilimi kamar yadda gwamnan Kano ya dauki gabarar taimaka musu ta kowanne hali don inganta rayuwarsu.
Sani Musa Danja ya lashin takobin hada kai da duk wata kungiya mai zaman kanta da daidaikun mutane don ganin sun tallafawa wannan yunkuri na shi na inganta rayuwar matasan jihar Kano.