Gwamnatin Kano ta dauki sabbin matakan kare Muhalli daga sauyin yanayi

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da daukar matakan da suka dace wajen yaki da sauyin yanayi domin magance gurbacewar muhalli.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24 a ranar Juma’a .

Shirin wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar, yana da manufar kare lafiyar jama’a, da rage hayaki mai gurbata muhalli da kuma samar da ci gaban tattalin arziki mai dorewa.

InShot 20250115 195118875
Talla

A yayin da ya ke mika kundin shirin ga gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, kwamishinan Muhalli da sauyin yanayi Dr. Dahiru Muhammad Hashim,ya ce shirin zai maida hankali wajen inganta aikin noma, da makamashi da Lafiya da Sufuri,Ilimi, da kuma haɓaka birane a Kano.

Gwamnatin Kano za ta ginawa masu lalurar laka cibiyar fasahar sadarwa

Dr. Hashim ya jaddada mahammcin mayar da hankali kan hanyoyin matsalolin sauyin yanayi na cikin gida, haɗin gwiwar kasashen duniya, ta hanyar samun tallafi daga kungiyoyin kasashen waje.

Gwamna Yusuf yace duka wannan na cikin manufofin gwamnatinsa na samar da Muhalli mai tsafta ga al’ummar Kano.

Ya ce a cikin shirin akwai manufar farfado da tattalin arziki da bunkasar harkokin kasuwanci da zuba jari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tallafawa al’umma: Kungiyar cigaban Unguwar Zango ta Karrama Dr. Muhammad Musa Zango

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Makaman Bichi Alhaji Isyaku Umar Tofa...

APC ta kori tsohon ministan Buhari

Jam'iyyar APC ta kori tsohon gwamnan jihar Osun kuma...

Babban Dalilin da ya sa na Shiga Siyasa – Sani Danja

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Mai baiwa gwamnan Kano shawara na...

Musa Iliyasu ya bayyana dalilin da yasa Kwankwaso ke neman komawa APC yanzu

Babban Daraktan kudi na hukumar raya kogunan Hadeja-Jama'are kuma...