Daga Ahmad Hamisu Gwale
Rahotanni sun bayyana akwai Iloli 10 da ficewar kasashen Sahel wato Burkina Faso, Mali, da Niger zasu fuskanta bayan sun fice daga kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Nahiyar Afrika ECOWAS.
Tun bayan ficewar kasashen Sahel wato Burkina Faso, Mali, da Nijar, farga ta bulla na yadda tattalin arzikin kasashen zai fuskanci koma baya.
Ga koma baya akalla 10 da kasashen za su fuskanta…..

1. Rasa fa’idar ciniki: Shakka babu Ƙasashen AES za su rasa damar yin amfani da yankin wajen yin ciniki tsakaninsu da kasashen ECOWAS, wanda zai sa fitar da kaya da shigo da kayayyaki su yi tsada a kasashen saboda karin kudin haraji a kan iyaka.
2. Kayyade amfani da tsarin Tattalin Arziki: Masu saka hannun jari na iya samun shakku na yin hulɗa da waɗannan ƙasashe saboda rashin tabbas, da kuma rage saka hannun jari kai tsaye daga ketare da raguwar ci gaban tattalin arziki.
3. Rashin samun walwala ta samun yanci: Al’umma daga Burkina Faso, Mali, da Nijar na iya fuskantar takunkumi na tafiye-tafiye a yammacin Afirka, wanda matuka hakan zai shafi kasuwanci, damar yin aiki, da haɗin gwiwa abubuwa masu yawa.
Gwamnatin Kano za ta ginawa masu lalurar laka cibiyar fasahar sadarwa
4. Karancin samun tsaro na bai daya:
Kasashen AES ba za su ci gajiyar shirin samar da tsaro da ECOWAS ke jagoranta ba, kamar rundunar yaki da ta’addanci a yankin, wanda zai bar su cikin mawuyacin hali na tada kayar baya.
5. Raguwa ta samun Tallafin kudi na Yankin: Kungiyar ECOWAS na bayar da tallafin kuɗi ga ƙasashe mambobinta, wanda a yanzu kuma ƙasashe ukun ba za su sake samun damar karbar kundin ba.
6. Kasashen zasu samu koma baya a harkokin Diflomasiyya:
Bayan da suka bar kungiyar hakan zai kawo musu cikas ga huldar diflomasiyya da kasashen da ke makwabtaka da su.
7. Fuskantar rashin gina kan iyaka domin amfanuwa : Ana iya cire ƙasashen AES daga ayyukan samar da ababen more rayuwa da ECOWAS ke tallafawa, gami da hanyoyi, layin dogo, da hanyoyin samar da makamashi.
8. Fargaba ta Tsaro: Akwai fargaba da Rashin zaman lafiya a kasashen AES, musamman ma da ake ci gaba da barazanar ta’addanci, na iya shiga cikin kasashe mambobin kungiyar ECOWAS, tare da kara fuskantar hadarin tsaron kan iyaka.
9. Koma baya, da rugujewar tattalin Arziki: Huldar kasuwanci za ta zo karshe tsakanin kasashen ECOWAS da kasashen na AES, wanda zai iya haifar da hauhawar farashin kaya da koma bayan tattalin arziki a yankunan.
kan iyaka.
10. Tsarin taimakon jin kai daga ECOWAS wanda ke da mahimmanci ga rayuwar al’ummar kasashe masu rauni na AES zai yi tasiri musamman yadda taimakon zai zo karshe.
Zuwa yanzu haka bayan da kasashen yankin Sahel na Burkina Faso, Mali da kuma Niger suka fita daga kungiyar ECOWAS, ficewarsu na nuni da kalubalen da ka iya shafar zaman lafiyarsu na dogon lokaci, da ci gaban tattalin arziki, da hadin gwiwar yankin da sauransu.