Dalilan da yasa aka dakatar da Bin Uthman daga limancin masallacin Sahaba

Date:

Masallacin Jami’ur Rahman, wanda a da ake kira da Masjid Sahaba, ya dakatar da Sheikh Muhammad Bin Uthman daga limanci biyo bayan hudubar da ya yi a ranar 24 ga watan Janairu.

Asalin masallacin, wanda Bin Uthman ke jagoranta tsawon shekaru 24, na kusa da sabon wanda AY Maikifi ya sayi filin.

InShot 20250115 195118875
Talla

Bayan Maikifi ya samu mallakar filin a hannun gwamnati don gina sabon masallacin Sahaba, sai ya tuntubi Bin Uthman inda suka amince da cewa tsohon masallacin Sahaba zai dawo sabon gini.

Sai dai kuma a yayin huɗubar da ya yi a ranar 24 ga watan Janairu, wacce ta haifar cece-ku-ce, Bin Uthman ya ba da labarin yadda aka rage masa matsayi wajen gudanar da harkokin masallacin.

Gwamnatin Kano ta dauki sabbin matakan kare Muhalli daga sauyin yanayi

A cewar sa, an nada shugabanni uku masallacin amma ba a nada shi a jagora ba.

Daily Nigerian ta gano cewa huɗubar ta ranar 24 ga watan Janairu ta fusata masallata, inda suka kusa dukan sakataren kwamitin amintattu na masallacin, Abdulkadir Isawa.

Hukumar kula da masallacin, a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun daraktan gudanarwa, ta ce ta dakatar da Bin Uthman har sai baba-ta-gani, tare da umartar shi da ya mika dukkan kayan masallacin da ke hannunsa.

A ranar Litinin ne kuma hukumar tsaro ta farin kaya, SSS, da majalisar malamai suka gayyaci Malam Bin Usman da wanda ya assasa sabon masallacin, Maikifi.

Hukumar SSS, a cewar majiyoyi, ta gargadi Bin Uthman kan huɗubar da su ka ce ka iya haifar da rikici ko hari a cikin masallacin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...