Tun bayan da majalisar dokokin jihar Kano ta sanar da yi wa ƙudurin kafa rundunar tsaro da gwamnatin jihar ta aike mata karatu na biyu, masana ke ta faman tsokaci dangane da hanyoyin da ya kamata a bi domin samun nasara.
Kano dai na fama da matsaloli irin na rikice-rikicen dabanci da ƙwacen waya, lamarin da ya yi sanadiyar ajalin mutane da dama.
Yadda tsarin rundunar zai kasance
Ɗan majalisar dokoki mai wakiltar ƙaramar hukumar Ƙiru, Abubakar Tasi’u Ƙiru, na cikin ƴan majalisar da suke goyon bayan ƙudurin, inda ya lissafa wasu abubuwan da ke ƙunshe a cikin ƙudurin kamar haka:
Rundunar tsaron ta jiha za ta kasance mai zaman kanta.
Kwamanda-Janar na jiha da ƙananan hukumomi ne za su jagoranci rundunar.
Jami’an rundunar na da ikon kama masu laifi su hannunta su ga ƴansanda domin gurfanar da su a gaban hukuma.
Jami’an rundunar na da damar amfani da bindigogi ƙirar gargajiya domin su kare kansu.
Dakarun za su yi ƙoƙari domin kauce wa shiga harkokin siyasa, domin za a zuba waɗanda ba ƴansiyasa ba.
Babu wanda za a ɗauka sai an tabbatar da nagartarsa da ingancinsa ba tun daga mahaifarsa, inda a cewarsa masu unguwanni da hakimai za su saka wa mutum hannu kafin a ɗauke shi domin gudun kar a ɗauki ɓatagari.
Zargin cin zarafi: Ƴansanda sun kama hadimin Gwamnan Kano
Hanyoyin samun nasara – Masanin tsaro
A game da wannan yunƙurin na kafa rundunar tsaron, BBC ta tuntuɓi masanin harkokin tsaro, Auwal Bala Durumin Iya, inda ya ce abin farin ciki ne, amma ya kamata a yi abin da ya dace.
“Samar da rundunar tsaro ta jihar Kano abu ne mai kyau idan ka kalli irin laifuffukan da ake yi a Kano. Hakan ya sa gwamnati ta ga ya dace ta yi tsarin da ya kamata domin samar da jami’an tsaro da za su taimaka wa jami’an tsaro na gwamnati tarayya domin tabbatar da tsaro a jihar Kano.”
Ya ce yanzu haka a nasa ɓangaren na masanin harkokin tsaro, yana gudanar da aikin horas da ƴan sa-kai daga ƙananan hukumomin Kano 44 domin koyar da su makamar aiki, domin su san yadda za su gudanar da aikin cikin ƙwarewa.
A game da batun cewa Kano ba ta fama da barazanar tsaro ta ƴanbindiga, Durumin Iya ya ce kowace jiha na da matsalar da take fuskanta.
“Kowace jiha akwai matakin da ya kamata ta ɗauka domin kare ƴan jiharta. Saboda haka Kano na da maƙwabtaka da jihohin da suke fama da matsalolin tsaro, saboda haka ba laifi idan Kano ta ɗauki mataki kafin matsalar ta kawo gare ta. Idan gemun ɗan’uwanka ya kamata da wuta, sai ka shafa wa naka ruwa ne,” in ji shi.
Sai dai ya ce akwai buƙatar a ɗauki waɗanda suka dace, kuma suke da ƙwarewa aiki da lungu da saƙon jihar.
A game da fargabar amfani da jami’an tsaron da ake yunƙurin kafawa wajen amfani da su domin muzguna wa abokan hamayya domin cin ribar siyasa, Durumin Iya ya ce komai yana da amfani da rashin amfaninsa.
“Amma amfanin samar da rundunar tsaron ya fi rashin amfaninsa. Ai ita gwamnati idan tana so ta yi amfani da jami’an tsaro, har na gwamnatin ma ana amfani da su. Kawai yana da kyau a zaƙulo waɗanda suka dace, sannan a tabbatar sun samu horo yadda ya dace.
“Ƴan sa-kai su ne suka daɗe suna aikin tsaro. Su ya kamata a ɗauka, a ƙara musu horo bayan wanda muka musu domin a wayar musu da kai kan tsame aikinsu daga siyasa da addini da ƙabilanci da duk wani abu da zai zama cin zarafin ɗan’adam.”
Ya ce ba za su zama kishiyar ƴansanda ba, kuma a cewarsa, ƴan sa-kai taimaka wa ƴansanda suke yi.
“Su jami’an tsaron ne za su taimaka wa ƴansanda da bayanan sirri, sannan akwai wurare da dama da ƴansanda ba sa iya shiga, sai ƴan sa-kai ne za su shiga su kamo musu masu laifin su kai musu,” in ji shi, sannan ya ƙara da cewa idan aka samun haɗin kai tsakanin ƴan sa-kai da ƴansanda, lallai za a samu ɗa mai ido.
Sai dai ya yi kira ga gwamnati da kada ta shigo da ƴansiyasa ciki lamarin, sannan ya yi kira ga ƴan jihar su ba jami’an tsaron goyon baya.
“Idan aka samu haɗin kai tsakanin mutanen gari da ƴansanda da ƴan sa-kai ɗin, to lallai muna fata matsalolin da ake fuskanta a wasu jihohi ba za su ƙaraso Kano ba. Za a cigaba da gudanar da harkokin kasuwanci da ibada cikin lumana,” in ji Durumin Iya.
Dabanci ne babbar matsalar Kano’
Yaya girman dabanci yake a Kano?
An haƙiƙance cewa babbar matsalar tsaron da ta fi damun birnin Kano ita ce dabanci wadda ita ce ke haddasa sauran laifuka irin su ƙwacen waya.
Daba wata matsala ce da aka daɗe ana fama da ita a jihar Kano da ke arewacin Najeriya inda tsawon shekaru ake ganin mummunan tasirinta.
Sai dai a kwanakin baya-bayan nan matsalar ta sake kunno kai inda a unguwar Ɗorayi faɗa tsakanin wasu ƴan daba ta kai ga kisan wani matashi.
Tuni dai rundunar ƴan sandan jihar Kano ta sanar da kama matashin tare da miƙa shi sashen da ke binciken manyan laifuka.
Matsalar ta daba dai ta sa jama’a a Kano na rayuwa cikin firgici tare da ƙaurace wa fitar dare da kuma yin taka tsan-tsan da rana kasancewar harin daba na iya ritsawa da mutum a kowane lokaci.
Duk da ƙoƙarin hukumomin tsaro wajen kawar da matsalar, al’umma na ci gaba da fuskantar ɗaurin kai ganin yadda matsalar ta ƙi ci ta ƙi cinyewa tsawon shekaru.
BBC ta tuntuɓi wani tubabben ɗan daba, Sagir Usman Yarima wanda ya bayyana cewa daba matsala ce gagaruma ganin yadda take ƙara muni da kuma kai wa ga kisan bil adama.
Ya ce a baya, akwai unguwannin da suka fi shahara da dabanci sai dai a yanzu, akwai wasu unguwannin da ke wajen tsakiyar birni da suka tsunduma cikin matsalar.
A cewarsa, matsalar ta fi yawa a tsakanin matasa waɗanda ake ganin su ne jagororin gobe.
Hakan na ƙara raunata irin gudummawar da matasan ya kamata a ce sun bayar wajen haɓaka jihar Kano ta ɓangarori da dama.
Sagir ya bayyana cewa harkar daba kamar makaranta ce inda ake da manyan malamai da ke da ɗalibai waɗanda su ne suka aikata miyagun laifuka bisa goyon bayan da suke samu.
Ya ce akwai manyan koma-baya da ke tattare da daba inda ya lissafo illolin da take yi kamar haka:
Ɗorayi
Chiranchi
Gama
Rimin Keɓe
‘Yankaba
Fanshekara
Sabon Titi
Hotoro
Sai kuma wasu unguwannin cikin ƙwaryar Kano da suka haɗa da:
Madigawa
Adakawa
Ƙoƙi
Dogon Nama
Yakasai
Fagge
Zage
Yalwa
Dan Agundi