Rahotanni na nuni da cewa wata tankar mai dauke da man fetur ta fashe a Kusogbogi dake karamar hukumar Agaie a jihar Neja.
Daily Trust ta ruwaito cewa wurin da lamarin ya faru iyaka ce tsakanin kananan hukumomin Agaie da Lapai.

Majiyoyi sun shaida wa wakilin Daily Trust cewa, ibtila’in ya faru ne a yau Talata amma ba a samu asarar rai ba.
Tafiyar Kwankwasiyya a wajena tamkar ibada ce – Abubakar Adamu Rano
Wani mazaunin Lapai, Malam Mahmud Abubakar, ya ce tankar ta fadi kuma ta kone kurmus a lokacin da ta ke kokarin wuce wata babbar mota.
Abubakar ya ci gaba da bayyana cewa wata tankar mai ma ta fashe a daidai wurin a makon da ya gabata.