Gwamnatin Kano da hadin gwiwar Kungiyar 9ja food za su koyawa masu bukata ta musamman sana’o’i

Date:

Daga Saminu Ibrahim Magashi.

Gwamnatin jihar kano ta sha alwashin tallafawa matasa kimanin dubu uku da kayaiyakin dogaro da kai.

Mai baiwa gwamnan Kano shawara kan harkokin matasa da wasanni Hon Sani Musa Danja wanda ya sami wakilcin TY Shaban shi ne ya bayyana hakan a yayin bikin kaddamar da shirin koyar da matasa sana’o’in dogaro dakai wanda wata kungiya mai zaman kanta mai suna 9ja food fiesta ta dauki nauyin koyar da matasan kyauta.

Sani Danja ya ce gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf tana da kudirin kawar da zaman kashe wanda a tsakanin matasan jihar Kano.

InShot 20250115 195118875
Talla

” A shirye muke mu hada kai da duk wata kungiya ko daidaikun al’umma don tabbatar da wannan Kudirin na mai girma gwamnan, domin matasa sune kashin bayan cigaban kowacce al’umma, don haka dole mu tsaya tsayin daka don inganta rayuwarsu”. A cewar Sani Danja

Mai baiwa gwamna shawara kan harkokin matasa da wasanni, za su cigaba da lalubo hanyoyi da za su taimaka wajen inganta rayuwar matasan jihar Kano.

“Gwamnatin mu a shirye take wurin tattara alkaluman masu bukata ta musamman ta yadda za a samu sanya su a harkokin gwamnatin tare da wayar da kansu dangane da illar barace-barace da kuma a basu tallafi da koya musu sano’oin da zasu iya rike kansu da basu tallafi da kuma tsarin komawarsu makaranta”. Inji shi

Gwamnan Kano ya nada mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai

Haka zalika ya ce akwai shirye-shiryen daga darajar filayen wasanni da sauya tasawirar su domin samun matasa masu cikakkiyar lafia da kwazo. Danja ya ce yana da niyyar kawo sabon tsari da zai kakkabe harkar daba shaye-shayen kwayoyi tare da koyar da su sana’o’in da za su iya rike kawunan su da taimakon yan’uwansu da mayar da wadan da suke da sha’awar komawa makaranta.

Ya yi alkawarin idan an kammala koyawa matasan sana’o’in da kungiyar ta dauki nauyi, ita kuma gwamnatin jihar Kano za ta baiwa matasan jari don su dogara da kawunansu.

Anasa bangaren shugaban kungiyar Muhammad Mustapha ya ce sun dauki nauyin koyawa matasan masu bukata ta musamman ne sana’o’i ne don kau da hankalinsu daga barace barace.

Ya kuma kara da cewa za su cigaba da hada kai da gwamnatin jihar Kano ta karkashin ofishin mai baiwa gwamnan Kano shawara na musamman kan harkokin matasa don aiwatar da wannan shirin na koyawa masu bukata ta musamman sana’o’in don su dogara da kawunansu.

Taron dai ya gudana ne a cikin tsohuwar jami’ar Bayero dake jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...