Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya ce zai jagoranci yiwa dan majalisarsu na tarayya Hon. Ali Sani Madakin Gini kiranye daga Majalisar , sakamakon al’ummar karamar Hukumar Dala da Kano basa bukatar wakilcinsa.
Kadaura24 ta rawaito Kwamared Waiya ya bayyana haka ne yayin taron masu ruwa da tsaki na karamar Hukumar Dala da Yan jamiyyar NNPP, Wanda aka gudanar a dakin taro na Mumbayya dake nan Kano.

Ya ce karamar Hukumar Dala tana bukatar jagora jajirtacce Wanda zai Kai matsalolin al’ummar yakin Majalisar wakilai domin a magance su.
Kaso 9.6% na daliban firamare a Kano suka iya karatu – UNICEF
Kwamishinan ya kuma godewa Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa tarin mukaman da ya baiwa wadanda suka fito daga karamar hukumar Dala.
Taron ya samu halartar Shugabannin jam’iyyar NNPP na karamar Hukumar Dala da sauran masu ruwa da tsaki na tafiyar Kwankwasiyya a karamar hukumar.