Maulidin Inyass: Kashim Shattima ya Jinjinawa Mabiya Darikar Tijjaniyya na Nigeria

Date:

Mataimakin shugaban Kasa Kashim Shattima ya yabawa mabiya darikar Tijjaniyya na Nigeria bisa yadda suke ba da gudunmawa wajen tabbatar da zamani lafiya a Nigeria.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24, ya ce Kashim Shattima ya bayyana hakan ne a jawabin da wakilinsa Alhaji Babagana Fannami ya gabatar a wajen taron Moulidin Shehu Ibrahim Inyass da aka gudanar a Kano.

Ya ce yan darikar Tijjaniyya sun jima suna ba da gudunmawa wajen tabbatar da zamani lafiya a Nigeria, inda yace yana fatan za su cigaba da yin hakan domin ya yi dai-dai da koyarwar addinin musulunci.

InShot 20250115 195118875
Talla

” Abubuwan da yan darikar Tijjaniyya suke yi na son zaman lafiya ya yi dai-dai da koyarwar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi wasallam, don haka ya yi kira da yan Nigeria da su rika yin koyi da son zaman lafiya irin na mabiya darikar Tijjaniyya”.

Da yake nasa jawabin gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf wanda shi ne mai masaukin baki, ya yaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya da mabiya darikar Tijjaniyya ke yi a Nigeria.

Maulidin Inyass: Sarkin Kano na 15 ya dauki nauyin karatun Matasa 30 a Jihar Bauchi

” A matsayina na mai masaukin ku, na yaba da yadda kuka zo Kano da ko ina a Nigeria domin halartar Maulidin Shehu Ibrahim Inyass a wannan jiha ta mu”. Inji Abba Kabir

A nasa jawabin sarkin Kano na 16 Khalifan Muhammad Sanusi II ya yi fatan mabiya darikar Tijjaniyya za su cigaba da yiwa Nigeria add’o’in samun zaman lafiya da karuwar arziki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...