Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana shirin farfado da tashar tireloli da aka yi watsi da su a shiyyar Kano ta Kudu.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya aikowa, gwamnan ya bayyana hakan ne biyo bayan ziyarar bazata da ya kai wurin dake Dakatsalle, daya daga cikin wuraren da aka yi watsi da aikin.
Sanarwar ta kara da cewa tun a shekarar 2014 ne aka fara gudanar da aikin tashar tirelolin a gwamnatin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, inda aka tsara tashar a wurare uku dake Dakatsalle, Gundutse, da Dawanau.

Sai dai kuma an yi watsi da ayyukan a lokacin gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamna Yusuf ya bayyana damuwarsa kan yadda ababen hawa ke yawan toshe hanyoyi, lamarin da ke kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa da kuma kawo cikas ga masu amfani da hanya a fadin birnin jihar.
Gwamna Kano ya kaddamar da aikin titi mai tsawon kilomita 5 a garin Dawakin Tofa
Gwamnan ya nanata kudirin gwamnatinsa na kammala aikin tashar tirelolin dake Dakatsalle da Gundutse don rage cunkoson ababen hawa, da bunkasa tattalin arziki a jihar.
Gwamnan ya yi Allah wadai da abin da gwamnatin da ta gabata ta yi, inda ya bayyana shi a matsayin barna da rashin kishin kasa.”
Ya soke duk wani fili da gwamnatin data gabata ta bayar a wuraren da za a yi tashar tirelolin.
Ya ba da tabbacin idan an kammala aikin za a mika tashar ga kungiyar masu harkokin sufuri NATO don cigaba da kula da wuraren.