Yadda Gwamnatin Kano ta yi Rinton Aiki a Dawakin Tofa – Bincike

Date:

A yan kwanakin nan gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf na cigaba da kaddamar da aiyukan tituna masu tsahon kilo mita 5 a wasu daga cikin kananan hukumomin jihar, wadanda gwamnatin da ya gada ta yi watsi da su saboda wasu dalilai da ake danganta su da siyasa.

Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito cewa tsohon gwamnan Kano Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso ne dai ya Fara gudunar da aikin titin a dukkanin kananan hukumomin jihar a karshen zangon mulkinsa na biyu.

A ranar litinin din nan ne gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da aikin titin a karamar hukumar dawakin Tofa.

InShot 20250115 195118875
Talla

A wajen bikin kaddamar da aikin titin da aka sanyawa fitulun titi masu amfani da hasken rana, mun jiyo gwamnan Abba Kabir Yusuf yana fadin cewa sun kammala aikin titin na Dawakin Tofa bayan da tsohuwar gwamnatin da ya gada ta yi watsi da titin tsahon shekaru 8, sannan sun banbanta aikin na Dawakin Tofa da na sauran kananan hukumomi saboda yadda titin ya kewaye cikin garin Dawakin Tofa domin inganta rayuwar al’ummar yankin.

Kadaura24 ta gudunar da bincike mai zurfi kan yadda wancan aikin titi na karamar hukumar Dawakin Tofa ya kasance ga kuma sakamakon bincike da muka gano.

Binciken ya nuna cewa tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya fara aikin kamar yadda aka yi a sauran kananan hukumomin jihar Kano 44.

Sai dai Kwankwaso bai kammala aikin ba wa’adin mulkinsa ya kare, amma kafin karewar mulkin na sa ga matakin da ya tafi ya bar aikin titin na karamar hukumar Dawakin Tofa yake kamar yadda wasu mazauna garin suka fadawa kadaura24.

Gwamna Kano ya kaddamar da aikin titi mai tsawon kilomita 5 a garin Dawakin Tofa

“Tsohon gwamnan Kano kwankwaso shi ne ya yi akalla kaso 18% na aikin titin domin shi ne ya fara sharewa da zuba kasa da kuma gina kwalbatoci a mafi yawancin titunan”.

“Hakan zalika Kwankwaso shi ne ya Biyan diyya ga masu gidaje da makarantu da masallatai da kuma shagunan dake kan titunan”.Inji wani mazaunin garin da ya nemi mu sakaye sunansa.

Bayan tafiyar gwamnatin Kwankwaso, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne ya karbi mulkin kano, kuma shi ne ya dora da wannan aikin .

Binciken mu ya nuna cewa Ganduje shi ne ya yi kusan kaso 80% aiyukan titi a cikin garin Dawakin Tofa, domin shi ne ya karasa sharewa da zuba kasa da gina kwalbatoci a sauran titunan.

A lokacinsa ne aka shimfida kwalta a dukkannin titunan da suka cikin garin Dawakin Tofa.

Haka zalika Ganduje ne fara sanya turakun wutar lantarki a titin farko na shiga garin.

Sannan kuma shi ne ya Gina kofofi 3 a kan wasu titunan, an kammala 1 saura 2.

Game da aiyukan da gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya gudanar kuwa a cikin garin Dawakin Tofa sun hadar da

1. Sanya fitulun Sola 231 a dukkanin titunan da wasu muhimman wurare.

2. Gyara/faffacewa da kwalta a wasu daga cikin wuraren na titunan da suka farfashe.

3. Gyara da siminti a saman wasu kwalbatoci da suka lalalce da kuma sanya musu da silab .

Wadannan shi ne aiyukan da gwamnan ya yi a cikin garin Dawakin Tofa, sannan gwamnan ya je garin ya kuma kaddamar da aikin.

Sai dai wasu daga cikin wadanda jaridar Kadaura24 ta tattauna da su a garin na Dawakin Tofa sun ce suna ganin kamar ko gwamnan ba shi da masaniya Kan matakin da aikin yake kafin ya fara aikinsa, ko kuma an ba shi abun a bai-bai.

Da fatan gwamnan zai bincika domin sanin hakikanin aikin da ya yi a garin don gudun Kar a rika yi masa wani irin kallo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...