Fadar Shugaban Ƙasa, ta musanta rahotannin da ke cewa ta tilasta wa tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ba da shaida a wata shari’ar sulhu da ke gudana a Paris.
Daily Trust a jiyan ne wata kafar labarai ta yanar gizo ta bayar da rahoton cewa an gayyaci tsohon Shugaba Buhari zuwa gaban kotu a Paris domin bayar da shaida kan shari’a da ta shafi rikicin kwangilar wutar lantarki ta Mambilla mai darajar dala biliyan 6.

Amma a cikin wata sanarwa , Bayo Onanuga, Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara Kan yada labarai, ya ce wannan ba gaskiya ba ne, sai dai kuma bai musanta cewa akai shari’ar ba.
Cikin sanarwar, Onanuga ya ce: “Fadar Shugaban Ƙasa ta samu labarin ƙarya da ke yawo a kafafen sada zumunta kan wata shari’a da ke gudana a Paris, inda Gwamnatin Najeriya ke cikin shari’ar.
A bai-bai aka fahimci kalaman da na yi akan gwamnatin Tinubu – Sarki Sanusi II
“Wannan shari’a ta sirri ce, wadda bai kamata ta fito fili a kafafen yada labarai ba, har sai masu yanke hukunci na ƙasa da ƙasa sun yanke hukunci.
“Duk da girmama sirrin wannan shari’a, muna son bayyanawa a fili cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai tilasta wa kowa yin shaida don goyon bayan Najeriya ko yin watsi da shaida a kan Najeriya ba.”