Waiya ya kaddamar da kungiyar wadanda za su rika tallata aiyukan gwamnatin Kano a Tiktok

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da masu amfani da manhajar Tiktok ( Kungiyar Kwankwasiyya Tiktokers) wadanda za su rika tallata aiyuka da manufofin gwamnatin Abba Kabir Yusuf.

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya jagorancin kaddamar da kwamitin a ofishinsa ranar lahadi.

Kwamared Waiya ya ce an kaddamar da kwamitin ne duba da irin tasirin da manhajar tiktok ta ke da shi a gurin Al,umma da kuma taimakawa matasa masu amfani da shafin don samar musu da abin yi .

InShot 20250115 195118875
Talla

“Na farko wadannan mutane za su tallata ayyukan gwamna Abba Kabir Yusuf, sannan kuma an samar masu aikin yi, kun ga min jefi tsuntsu biyu sa dotse biyu”.

Ya ce zasu hada kai da kwararru a fannin fasahar zamani domin su ba su horo na musamman domin su san damarun isar da sako a manhajar ta Tiktok.

Kwamishina Waiya ya karbi bakuncin Shugabannin Jaridar Daily trust

Da yake jawabi sabon shugaban kungiyar Shamsudden Abdullahi Sani ya godewa kwamishinan, sannan ya ba da tabbacin zasu yi aiki tukuru domin tallata aiyukan gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf.

Tabbas Gwamnatin jihar Kano tana aikin da ya kamata, mu kuma za su tsaya tsayin taka domin tallatawa da kuma wayar da akan al’umma kan manufofin gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...