Wasu ya’yan kungiyar NNPP Kwankwasiyya Media Forum sun kai takardar korafi ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC da hukumar karbar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano, bisa zargin wasu jami’an gwamnatin Kano da shugaban kungiyar da rashin adalci wajen rabon kudaden da gwamnan Kano ya basu domin rabawa yan kungiyar.
A wata wasika mai dauke da sa hannun Muji Sigan Jingau da Labaran Bage da Zaharadden Kabara, Alhaji. Isa Abdullahi da kuma Rabi’u Eme yakasai, sun bukaci hukumomin biyu da gudunar da bincike domin gano yadda aka kashe Naira Miliyan 30 da gwamnan Kano ya basu domin tallafawa ya’yan kungiyar.

” Da jin mu, mun jiyo gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a ranar 5 ga watan Janairu, 2024, a dakin taro na Coronation dake gidan gwamnatin Kano, inda gwamnan ya ce na baku Naira Miliyan 30 domin ku tallafawa ya’yan kungiyar NNPP Kwankwasiyya Media Forum don rage musu radadin halin da ake ciki”.
Da dumi-dumi: Baffa Babba ya yiwa Kofa Martani Kan sulhunta Kwankwaso da Ganduje
“Cikin kudaden da gwamnan ya baya ya zuwa yanzu babu ko sisin kobo a Asusun kungiyar, kuma wasu mutane 4 Alhajiji Nagoda ( SS Media) da Samaila Murtala Zawa’i ( SSA Media) da Shugaban kungiyar Nura Bakwankwashe da sakataren kungiyar Ali gyara Hausawa su muke zargi sun raba kudi da babura ga wadanda suke so, ba tare da yin adalci ba”.
Wasikar mai dauke da kwanan watan 16 ga watan Janairu, 2024, masu koken sun roki hukumomin da su binciki lamarin domin tabbatar da anyi adalci ga kowa.
Kadaura24 dai ta ga wasikar da ke nuni da cewa dukkanin hukumomin biyu sun karbi korafin na mutanen 8 da Suka ce su yan kungiyar NNPP Kwankwasiyya Media Forum ne.