Abun da ya jawo barkewar cutar murar tsuntsaye a Kano – Kwamishinan lafiya

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Yayin da ake fargabar samun ɓarkewar annobar murar tsuntsaye a Kano, gwamnatin jihar ta buƙaci al’umma da su kwantar da hankalinsu tare da kai rahoton duk wani zargi da ake da shi game da cutar ga hukumomin da abin ya shafa.

Raɗe-raɗin ɓullar annobar ya bayyana ne sakamakon wani rahoton da aka samu a watan Disamba na 2024 cewa wani matashi ɗan ƙaramar hukumar Gwale ya sayo agwagwa a kasuwar Janguza da ke ƙaramar hukumar Tofa ya haɗa ta da kajin da yake kiwo.

Daga baya sai ya lura kajin sun fara nuna alamun matsalar numfashi da har ta kai 35 cikin 50 sun mutu. Hakan ya sa ya kai wasu daga cikin waɗanda suka mutu asibitin dabbobi na Gwale domin yin bincike, inda a makon farko na watan Janairun 2025 sakamakon binciken ya nuna murar tsuntsaye ce ta yi sanadin mutuwar tasu.

Talla

Samun sakamakon binciken ke da wuya, sai ma’aikatar noma ta je ta kulle wurin da mutumin ke yin kiwon tare da kashe ragowar kajin da yi wa wurin baki ɗaya feshin magani. Haka kuma, ma’aikatar ta yi irin wannan feshin a wurin da ake sayar da kaji a kasuwar Janguza tare da wayar wa masu sana’ar kai game da illar murar tsuntsaye.

Da tsokaci game da haka, a yau, Kwamishinan Lafiya, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, a cikin wata sanarwar manema labarai da jami’in hulɗa da jama’a na ma’aikatar Ibrahim Abdullahi ya aikowa Kadaura24, ya buƙaci jama’ar jihar nan da su kwantar da hankalinsu saboda lamarin bai kai a kira shi ɓarkewar annoba ba.

Gwamnatin Kano za ta kirkiri tsarin tattaunawa da al’umma don jin matsalolinsu – Waiya

Kwamishinan ya ce ma’aikatar lafiya na tsaye sosai a kan al’amarin, tana da ɗaukar dukkan matakan da suka dace na tunkarar matsalar domin daƙile tasirinta kafin ta zama barazana.

Dakta Labaran ya ce kasancewar cutar murar tsuntsaye na harbar mutum tare da haddasa illa ga jiki ya sanya ya kira taro da kwamitocin Kar-ta-Kwana da na Lafiya Guda Ɗaya (Emergency Preparedness Response da One Health) da ke da wakilcin ma’aikatun noma, muhalli da albarkatun ruwa da kuma ƙungiyoyin ci-gaba domin a tattauna tare da tsara hanyoyin da za a tunkari al’amarin.

Ya ce, “Wannan shi muke yi a halin yanzu. Za a rinƙa yin taro da masu ruwa da tsaki a kowane mako. Za a rinƙa sanar da al’umma a kai a kai halin da ake ci game da cutar.

“Za a ƙarfafa sa ido a kowace ƙaramar hukuma, musamman tsakanin masu kiwon kaji da sauran tsuntsaye, sannan za a rinƙa bai wa waɗannan kwamitoci rahoto a kowace rana tare da sanar da Gwamna Abba Kabir Yusuf halin da ake ciki.”

Kwamishinan ya ce alamomin cutar sun haɗa da zazzaɓi, fitar da majina, jan-ido da sauransu, inda ya buƙaci al’umma musamman masu kiwon kaji da su zama jami’an sa ido na farko saboda su kare ababen da suke kiwo da dukiyoyinsu, tare da kai rahoton duk wani yanayi da ke hana kajin walwala ga hukumomin da suka dace domin ɗaukar mataki a kan lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Naja’atu Muhd ta mayarwa da Nuhu Ribado Martani Kan barazanar da ya yi mata

Daga Isa Ahmad Getso   Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja'atu Muhammad...

Zargin Sharrin: Ribado ya yi barazanar maka Naja Muhammad a Kotu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mai baiwa shugaban kasa shawara kan...

Rusau: Kwankwaso ya bukaci gwamnan Kano ya biya diyyar mutanen da aka kashe a Rimin Zakara

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano,...

Za mu karawa Limamai, Ladanai da Na’ibansu alawus na wata-wata – Shugaban Karamar hukumar Dala

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Suraj...