Gwamnatin Kano za ta kirkiri tsarin tattaunawa da al’umma don jin matsalolinsu – Waiya

Date:

Daga Sidiya Abubakar

 

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta kirkiri wani tsari na musamman da gwamnan za ta rinka tattaunawa da al’umma kai tsaye dan jin matsalolin su tare da karbar shawarwari daga garesu.

Kwamishinan yada labarai Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kwamatin da gwamnan Kano ya kafa dan bincikar musabbabin rikice rikicen da aka samu lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a watan August shekarar da ta gabata ta 2024 a nan Kano.

Talla

A wata sanarwa da hadimin kwamishinan kan harkokin yada labarai Bashir A Bashir ya aikowa Kadaura24, ya ce Waiya ya kuma ce kowanne kwamishina da shugabannin ma’aikatu za su kasance a wajen taron tattaunawar danjin shawarwari da kuma koken da mutane ke dasu a ma’aikatun su.

Ya kuma ce hakan zai sa gwamnati ta san irin matsalolin dake damun al’umma kai tsaye.

Ɗan takarar Sanata a NNPP ya fice daga Jam’iyyar

Da yake jawabi shugaban kwamatin Justice Lawan Wada Muhammad mai Ritaya, da Farfesa Muhammad M Barodo yai magana a madadinsa cewa ya yi sun zo gun kwamishinan ne domin ta yashi murna kan mukamin da aka bashi.

Ya kuma ce idan har akai amfani da kudurorin da kwamishinan yazo da shi za a samu ci gaba ta fannini da dama a jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...