Tsohon dan takarar Sanata na jam’iyyar NNPP a jihar Borno, Atom Magira ya fice daga jam’iyyar zuwa ta Social Democratic Party, SDP.
Magira wanda tsohon dan takarar gwamna ne a karkashin jam’iyyar APC, shi ake ganin a matsayin jagoran jam’iyyun adawa a jihar.

A kwananan dai aka kama shi kuma aka tsare shi a gidan yari saboda kiran da ya yi na neman ‘yan siyasa da su yi hadaka (Maja) a jam’iyyar adawa daya a jihar da kuma zarginsa da sukar Gwamna Babagana Umara Zulum.