Sabon Kwamishinan Ƙananan Hukumomi na jihar Kano, Alhaji Tajuddin Usman ya mayar da Naira miliyan 100 ga asusun gwamnatin jihar.
Usman ya mayar da kuɗin ne na rarar kuɗaɗen kwangilar dinka tufafin makaranta ga ɗaliban firamare dubu 789 a fadin ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Kwamishinan, wanda shi ne shugaban kwamitin raba kayan, ya mayar da rarar kudaden da aka ware domin ɗinkawa daliban firamare sabbin tufafin makaranta, inda kuɗaɗen su ka yi ragowa bayan da aka kammala aiki kuma shugaban kwamatin ya kuma dawo dasu.
Rahma Radio ta rawaito cewa Usman ya bayyana hakan yayin kaddamar da rabon kayan a gidan gwamnatin Kano a jiya Litinin.