Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Gwamnatin jihar Kano ta ce daga yanzu wajibi ne kowacce motar haya ta kasance akwai kwandon zuba shara a cikinta domin amfanin fasinjoji.
Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar, Dahiru Muhammed Hashim, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da shirin tsaftace Kasuwar Kwari bisa haɗin guiwar ma’aikatarsa da ta sufuri, da ta kasuwanci da masana’antu.

Har ila yau, shirin ya sake dawo da masu sharar tituna wadanda aka raba su zuwa wurare daban-daban na manyan titunan birnin Kano
Da yake jawabi a lokacin kaddamar da shirin, kwamishinan ya ce hakan ya nuna jajircewar gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, na ganin jihar Kano ta kasance mafi tsafta, lafiya, da kare muhalli ga daukacin mazauna jihar baki daya.
Da dumi-dumi: Bayan tsige Kakakinta Majalisar dokokin Lagos ta zabi sabuwar shugabar majalisar
“Tsaftar muhalli wani bangare ne na kiwon lafiyar jama’a da ci gaban kowanne birni domin kawata shi.
Gwamnatin jihar Kano ba zata lamunci zubar da sha a ko’ina ba, hakan tasa muka dawo da dokar sanya kwanduna a motocin haya domin kawar da duk wani datti a kan tutuna.
Ya nanata kudirin gwamnatin Kano na ganin an inganta muhalli domin shi ne ginshikin kiwon lafiya da inganta burane da kuma kawata birnin Kano.