Mojisola Meranda ta zama sabuwar shugabar majalisar dokokin jihar Legas bayan tsige Mudashiru Obasa daga mukamin.
Kafin ta zama shugabar majalisar, Meranda ita ce mataimakiyar kakakin majalisar.
Meranta ta zama shugabar majalisar dokokin jihar ne biyo bayan tsige Mudashiru Obasa a matsayin shugaban majalisar saboda zargin rashin da’a da kuma cin zarafi.

SaharaReporters ta ruwaito a watan Disamba 2024 cewa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta shigar da kara domin ta binciki Obasa kan zargin karkatar da kudi, da cin amanar jama’a, da kuma cin zarafi.
Rubabbun yan Kwankwasiyya Sanata Barau yake karba – MD Radio
Wata kara da kungiyar Progressive Youth Movement na Ikeja, jihar Legas ta shigar, ta zargi Obasa da yin amfani da wasu kamfanoni wajen wawure kudaden majalisar dokokin Legas da kuma saba ka’idojin saye da sayarwa.
Kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta bukaci EFCC ta binciki majalisar dokokin Legas kan amfani da Naira biliyan 17 wajen gina kofar gida.