Kotun daukaka kara dake zaman ta a Abuja ta yanke hukuncin cewa babbar kotun tarayya ba ta da hurumin saurarar duk wata kara da ta shafi dokar masarautu.
Haka zalika kotun ta ce sashi na 251 na kundin tsarin mulkin Nigeria ya yayi bayani dalla-dalla kan harancin kotun tarayya ta shiga al’amarin da ya masarautu.
Majiyar Kadaura24 ta Justice watch ta rawaito Batun tauye hakkin dan Adam kuwa Kotun daukaka karar ta ce Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya gaza gabatar da hujjojin da za su gasgata da’awarsa.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito ce Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero bayan da gwamnatinsa Kano ta ayyana cire shi, ya garzaya gaban babbar kotun tarayya dake Kano domin kalubalantar matakin gwamnatin.
Aminu Ado Bayero yana da’awar cewa an take masa hakkinsa a matsayinsa na dan adam, don haka yake neman kotun da duba labarin, sai dai gwamnatin Kano ta ce kotun tarayyar bata da hurumin saurarar kara lamarin da yasa ta tafi kotun daukaka kara domin nemo fassara.
Kotun daukaka Karar ta ce Babbar kotun tarayyar ba ta da hurumin kamar yadda kotun koli ta Kasa ta taba yanke hukuncin akan shari’ar Tukur da gwamnan gongola.
Kotun ta ce kotun da ke da hurumin shari’ar masarautu a tsarin mulkin Nigeria, ita ce babbar kotun jiha ce ba babbar kotun tarayya ba,