Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya zargi tsohon gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da kin biyan yan fasho hakkokinsu tsahon shekaru 8 wanda hakan ya jawo talauci jihar.
Ya ce sakacin gwamnatin Ganduje na kin biyan yan fasho da wadanda suka mutu a bakin aiki ne ya jawo suka biyo gwamnatin Kano kudaden da yawansu ya kai biliyan 48.

Gwamnan Yusuf ya yi wannan zargin ne lokacin da yake jawabi a wajen kaddamar da biyan yan fasho hakkokinsu kashi na uku, a aka sake ware musu Naira Biliyan 5 domin rage basussukan da suke bin gwamnati.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24, yace gwamnan ya tausayawa yan fashon saboda bakar wahalar da suka sha a tsahon shekaru 8 na mulkin Ganduje.
A karon farko bayan cire shi daga sakataren gwamnatin Kano Baffa Bichi ya Magantu
Yace biyan akalla Naira biliyan 16 ga yan fasho kimanin 6,886 na daga kokarinsa na cika alkawuran da ya yi lokacin yakin neman zaben 2023. Inda ya ba da tabbacin zai cigaba da biyan hakkokinsu don inganta rayuwarsu.
Gwamna Yusuf ya kuma yi amfani da bikin wajen sanar da karin kudin fansho na wata-wata daga Naira dubu 5 zuwa Naira dubu 20. Ya ce ya yi hakan ne saboda yadda kayan masarufi ya tashi rayuwa kuma ta yi tsada.
Tun da farko a jawabinsa shugaban kungiyar Malamai ta Kasa Com. Titus Audu Amba, ya yabawa gwamnan bisa biyan hakkokin wadanda suka ga aiki da wadanda suka riga mu gidan Gaskiya.