Fassarar Binciken Mohammed Dahiru Lawal
Ikirari: Wani mai yin gajerun bidiyon barkwanci—Bello Galadanci, wanda aka fi sani da Dan Bello, ya yi ikirarin cewa Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta soke jarabawar karin girma—wacce ta shirya wa jami’anta a shekarar 2024 saboda zargin yin magudi daga jami’ai daga yankin arewa, bisa umarnin Shugaban Hukumar Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi.
Bayani: A watan Disamba 2024, jaridar PRNigeria ta bayar da rahoton cewa majalisar gudanarwa ta Hukumar Kwastam—wato Nigeria Customs Service Board, ta amince da karin girma ga kananan jami’ai 1,419 a matakai daban-daban. Wannan matakin ya samu amincewa ne a taron shugabanci karo na goma da Shugaban Hukumar Kwastam, CGC Bashir Adewale Adeniyi, ya jagoranta a ranar 29 ga Nuwamba, 2024.
Jim kadan bayan daukar wannan mataki, sai shugaban Majalisar Gudanarwa na Hukumar Kwastam ta kasa (NCSB), karkashin jagorancin Ministan Kudi, Mr. Wale Edun, ta tabbatar da nadin Mataimakin Kwamturola-Janar (DCG) da Mataimakan Kwamturola-Janar guda bakwai (ACGs). Har ila yau, an kara wa manyan jami’ai 4,291 girma.
A cikin wannan watan na Disamba dai, Hukumar Kwastam ta sanar da shirin daukar aiki na jami’ai 3,927 bayan ta bayar da karin girma na musamman da samun kudin shiga sama da Naira tiriliyan biyar a 2024. Amma har kafin sakin gajeren bidiyon da Dan Bello yayi, ba bu wata alamar rashin jin dadi kan tsarin karin girma daga kowa.
Tabbatarwa: Jaridar PRNigeria ta tuntubi majiyoyi da dama daga Shalkwatar Hukumar Kwastam dake Birnin Abuja. Majiyoyin sun tabbatar da cewa an gudanar da jarabawar karin girma a duk faɗin shiyyoyin Nijeriya, amma an soke wani sashe sabida gano wadansu matsaloli da aka yi—wanda daga bisani kuma aka sake shirya wata jarabawar, inda aka gudanar da ita cikin adalci, aka bai wa dukkan jami’an da abin ya shafa damar shiga.
Jarabawar da ta shafi karin girma daga mukaman Superintendent of Customs (SC) zuwa Chief Superintendent of Customs (CSC) an fara gudanar da ita ne a ranar 20 ga Agusta, 2024, a wurare biyar: Abuja, Kaduna, Bauchi, Legas, da Fatakwal. Sabida matsalolin da aka gano, an sake jadawalin jarabawar zuwa ranar 8 ga Nuwamba, 2024, a Abuja da Legas, inda aka sanya ido sosai kan gudanarwar jarabawar.
A karon farko bayan cire shi daga sakataren gwamnatin Kano Baffa Bichi ya Magantu
Wata takarda da jaridar PRNigeria ta samo ta nuna yadda aka raba karin girman bisa cancanta tsakanin yankunan kasar. Daga cikin jami’ai 642 da aka kara wa girma daga SC zuwa CSC, ga yadda aka raba su:
Arewa ta Tsakiya: 122
Arewa maso Gabas: 100
Arewa maso Yamma: 152
Kudu maso Gabas: 78
Kudu maso Kudu: 106
Kudu maso Yamma: 84
Jimilla, jami’ai 374 daga Arewa (58%) aka kara wa girma, yayin da daga Kudu aka samu jami’ai 268 (42%).
Haka zalika, daga cikin jami’ai 16 da aka ba su karin girma na musamman saboda bajinta da jarunta, tara (9) sun fito daga Arewa. Wasu jami’ai biyu na musamman daga Kano sun samu karin girma sau biyu.
Martanin Jami’ai daga Arewa: Wadansu manyan jami’an Hukumar Kwastam daga Arewa, yayin zantawa da PRNigeria, sun musanta zargin nuna bambancin kabilanci. Sun jaddada cewa CGC Bashir Adewale Adeniyi yana bin ka’idar adalci kuma yana tabbatar da cewa karin girma ya kasance bisa cancanta.
“Shugaban Hukumar Kwastam namu yana aiki ne bisa cancanta da kwarewa. Maganganun nuna bangaranci a kafafen sada zumunta suna da hatsarin kawo rashin hadin kai a hukumar NCS,” in ji wani jami’i.
Wani jami’i ya bayyana yadda CGC ke tafiyar da hukumar cikin hadin kai, yana bai wa kowa damar taka rawa, har da nada shugabanni daga Arewa a hedikwata:
Mataimakin Kwamptrola-Janar (DCG) Bello Jibo, mai kula da Harkokin Gudanarwa da Kudi, daga Jihar Kebbi.
DCG Caroline N., mai kula da Harkokin Kudaden Shiga, daga Filato.
Shugaban Ma’aikata Isa Umar, daga Zamfara.
Kakakin Hujumar na Kasa Abdullahi Aliyu Maiwada, daga Katsina.
Sakataren Kudi Adamu Yusuf Musa, daga Bauchi.
ADC Datuhun James, daga Filato.
Direbobi da masu tsaron lafiyarsa daga jihohi daban-daban na Arewa, kamar Sokoto, Kano, da Kogi.
“Salon shugabancin CG yana nuna bambancin kabilanci ba shi da tasiri a ayyukansa. Zargin nuna bangaranci ba su da tushe,” wani jami’i ya bayyana.
Kammalawa: Binciken PRNigeria ya nuna cewa jarabawar karin girma an soke ta ne saboda matsalolin da aka gano, ba don nuna bambanci ba. Dukkan jami’an da abin ya shafa sun samu damar sake rubuta jarabawar. Bayanai daga karin girman sun nuna cewa an bi tsarin adalci da cancanta, inda jami’ai daga Arewa suka samu karin kaso mai yawa.
Hukunci: Binciken PRNigeria ya nuna babu wani shaida da ke nuna cewa an nuna bambanci wajen karin girma ko dakatar da mukamai ga jami’ai daga Arewa. Don haka, zargin yaudara ne kuma ba gaskiya ba.