Ku duniya ta ke yayi, dole mu hada kai wajen yada manufofin gwamnatin Kano – Waiya ga yan jaridun yanar gizo

Date:

 

Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na hada kai da kafafen yada labarai na yanar gizo domin yada kudirori da manufofinta don sanar da duniya aiyukan da take yiwa al’umma .

” A wannan zamani ku duniya take yayi, domin suke abu zai faru yanzu-yanzu ku yada shi ga al’umma, amma sai dai akwai bukatar mu hada kai da ku wajen yakar masu yada labaran karya domin wannan al’amarin yana damun al’umma”. Inji Waiya

Sabon Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan a wata ganawa da yi da Kungiyar Mawallafa Jaridun Yanar Gizo (Association of Online Media Guild ASSOMEG) a fishinsa.

Talla

” Dani ni abokin yan jaridu ne yanzu kuma gwamnan Yusuf ya bani wannan mukamin don haka dole mu hada hannu waje guda da ku domin yada manufofin gwamnatin Kano, don haka Ina neman hadin kan ku, kuma Ina baku tabbacin za mu yi aiki tare”. A cewar Kwamishina Waiya

Kwamishinan ya jaddada bukatar yin tsari da hadin gwiwa da kafafen yada labarai na yanar gizo don tabbatar da yada sahihin ayyuka da manufofin gwamnati.

Gwamnati ta aiwatar da ayyuka da yawa, kuma suna bukatar a yada su. ” in ji shi.

A karon farko bayan cire shi daga sakataren gwamnatin Kano Baffa Bichi ya Magantu

Kwamishinan ya kuma yi kira da a hada kai a tsakanin ‘yan jarida na yanar gizo a Kano tare da bayyana shirin horas da dukkanin jami’an yada labarai da jami’an hulda da jama’a na jihar kan tsarin yada Labarai na zamani.

A nasa bangaren, Shugaban Kungiyar Mawallafa Jaridun Yanar Gizo ta The Association of Online Media Guild ASSOMEG Abdullateef Abubakar Jos, ya bayyana goyon bayansa ga yadda Kwamishinan ya ke mu’amalantar kafafen yada labarai.

“Mambobinmu kwararru ne, mun zo nan don taya ka murna, kuma muna goyon bayan matakin da ka dauka na kokarin hiras da ma’aikatanka wanda hakan zai taima wajen inganta harkokin yada labarai a Kano.” inji shi.

Abubakar Jos ya jaddada bukatar duba lamarin labaran bogi da kuma magance matsalar, wanda ya ce tana yin illa mai yawa ga kowacce gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

A karon farko bayan cire shi daga sakataren gwamnatin Kano Baffa Bichi ya Magantu

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano Dr....

Gwamna Yusuf ya biya biliyan 16 ga yan fansho a Kano

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jaddada...

Dr. Danmaraya Ya Fara Shirin Sauya Fasalin Ma’aikatar Kudi ta Kano

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan harkokin kudi na jihar Kano,...

2027: Gwamnan Kano Ya Yiwa Ganduje, Abdullahi Abbas Martani

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi...