Gwamnan Kano ya tsawaita wa’adin Aiki ga Shugaban ma’aikata, da wasu manyan sakatarori

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kara wa’adin aiki na tsahon Shekaru 2 ga shugaban ma’aikatan gwamnati, da wasu manyan sakatarorin gwamnatin da kuma wasu manyan ma’aikatan gwamnati daga ranar 31 ga Disamba 2024.

Hakan na kunshe ne a cikin wani umarni na zartaswa da Gwamna ya sanya wa hannu .

Gwamnan ya dauki wannan matakin ne bisa dogaro ga sashi na 5 (2) da 208 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999 .

Wadanda Karin wa’adin shekaru biyun ya shafa sun hada da Alhaji Abdullahi Musa a matsayin shugaban ma’aikatan gwamnati, Umar Muhammad Jalo, Bilkisu Shehu Maimota, Mu’azatu Isa Dutse, Abdulmuminu Musa, da Tijjani Muhammad Sharif a matsayin manyan sakatarori sai Bashir Idris Diso a matsayin magatakarda na ofishin. majalisar dokokin jihar.

Talla

Idan za a iya tunawa, ma’aikatan da wannan karin wa’adin ya shafa ta hanyar bin dokokin hukumar kula da fansho ta jihar Kano, za su yi ritaya ne a ranar 31 ga Disamba, 2024.

Hakazalika Gwamnan ya kuma kara wa wasu manyan ma’aikatan gwamnati wa’adin aiki na tsawon shekaru biyu da suka hada da Comrade Kabiru Ado Minjibir da Kwamared Marwan Mustapha da Kwamared Tajuddeen Bashir Baba da Kwamared Hashim A. Sule da kuma Kwamared Kabiru inuwa.

Gwamnatin Kano ta fara kwashe yaran da ke gararamba kan titunan jihar

Sauran sun hada da Others are Amina Idris, Psychiatric Nurse, Ahmad Lawan, Peri-Operative Nurse , Hussaini Nuhu Pediatric Nurse , Salisu H. Nadosun Peri-Operative Nurse da Larai Ahmadu Nurse Care, wadanda dukkanin su sun fito ne daga bangaren lafiya .

A wata sanarwa da daraktan wayar da kai na Ofishin shugaban ma’aikata Aliyu Yusuf ya fitar ya ce an umurci duk wadanda suka ci gajiyar wannan karin wa’adi da su ci gaba da tafiyar da ayyukan ofishin da aka tura shi kamar yadda dokar ma’aikata ta tanada .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...