Jerin Aiyuka 24 da Abdulmumini Kofa ya yi a kananan hukumomin Kiru da Bebeji a 2024

Date:

Daga Zakaria Adam Jigirya

 

A cikin shekarar ta 2024 da muka yi bankwana da ita Dan majalisar tarayya mai wakilar kananan hukumomin Kiru da babeji Abdulmumini Jibrin Kofa ya guda da muhimman aiyukan raya kasa da cigaban al’ummar da yake wakilta.

Hausawa su kance, Juma’ar da zata yi kyau tun daga Laraba ake ganeta. Hakika kyakykyawan fatan da muke da shi akan Hon Kofa kullum kara tabbata yake.

A cikin watanni goma sha biyu na wannan shekarar Hon Kofa ya yi wasu aikace-aikace tare da tallafi ga al’ummar wannan yanki namu mai albarka.

Talla

Ga wasu a cikin misalan kamar haka:

1. A farkon shekaran nan Hon Kofa ya bada zunzurutun kudi har milyan goma a matsayin tallafin karatu ga daliban Kiru/Bebeji.

2. Hon Kofa ya yi tallafin kayan haihuwa ga mata masu juna biyu a Kiru/Bebeji.

3. Hon Kofa ya raba shinkafa dubu biyu da dari uku a lokacin azumi. Kudinta ya haura Naira milyan dari.

4. Hon Kofa ya gina block mai dauke da aji biyu a mazabar Kofa.

5. Hon Kofa ya gina block dauke da aji biyu a mazabar Zuwo.

6. Hon Kofa ya gina block mai dauke da aji biyu a garin tariwa.

7. Hon Kofa ya gina makaranta mai azujuwa shida a Bebeji Model Primary School a mazabar Bebeji.

8. A cikin wannan shekarar kadai Hon Kofa ya samar da fitulu masu amfani da hasken rana sama da dari bakwai. Bebeji, Tariwa, Baguda, Gargai, Kuki, Gwarmai, Ranka, Durmawa daga karamar hukumar Bebeji, sai Bargoni, Baawa, Yako, Badafi, Yalwa, da Zuwo na daga cikin wanda suka fara amfana da kashin farko a wannan shekarar.
Ragowar dukkan mazabun Kiru/Bebeji wanda ban ambata ba suma yanzu dukkansu ana nan ana aikin sanya musu irin wannan fitulun.

Manufofi 4 da nake son cimma a matsayin shugaban raya kogunan Hadejia – Jama’are – Rabi’u Sulaiman Bichi

9. Hon Kofa ya rabawa manoma taki Urea da Kamfa buhu dari bakwai a lokacin damuna a matsayin tallafi.

10. Hon Kofa ya samar da rijiyar burtsatsa mai amfani da hasken rana a mazabar Durmawa.

11. Hon Kofa ya samar da irin wannan rijiya a garin Yako.

12. Hon Kofa ya samar da rijiyar burtsatse a garin Damau da Kogo.
13. Hon Kofa ya samawa wasu matasa aikin Technical Aids Corp, wanda a yanzu haka suna kasar Guinea.

14. Hon Kofa ya kara raba shinkafa a karo na biyu domin ragewa al’uma radadin da suke ciki buhu 1300 duka 50kg wanda itama kudinta ya haura milyan dari.

15. Hon Kofa ya kara samo gine-ginen blocks masu aji biyu, inda ya kara daukar guda biyar sukutum ya kara kaiwa mazabar Bebeji domin samarwa wata makaranta mutsuguni da dundundun.

16. Ya kuma debi wasu guda biyar din ya kaisu mazabar yalwa domin fadada wata makaranta dake fama da matsalar azujuwa.

17. Hon Kofa ya samo rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana, inda ake gina guda hudu a mazabar Bebeji.

18. An kuma samar da ita wannan rijiya mai amfani da hasken rana a garin Kwanar Dangora.

19. Hon Kofa ya karawa mazabar Kiru da rijoyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana guda hudu.

20. Hon Kofa ya samar da wajen noma na zamani a garin Kofa tare da rijiyar mai amfani da hasken rana.

21. Hon Kofa ya bada aikin gyaran wasu azujuwa a makarantun Dansoshiya, Gabari, Baawa, Badafi, Rahama, Bebeji.

22. Ya kuma bada gyaran wata makaranta a garin Kofa GASS KOFA a kan kudi milyan Goma.

23. Ya kuma bada gyaran wasu blocks a Kofa Central Primary School.

24. Ya kuma bawa kwamatin koli Naira Milyan ashirin domin yin gyare-gyaren borehole a Kiru/Bebeji, wanda ana sa ran a kalla rijiyoyin burtsatse sama da dari wanda suka lalace za’a gyara su a lungu da sako na Kiru/Bebeji.

Wannan fa wasu daga cikin ayyuka da tallafi da Hon Kofa ya yi ne a cikin wannan shekara da muke bankwana da ita. Ina kuma yi mana albishir cikin yardar Allah a cikin wannan shekara da zamu shiga akwai ayyuka wanda suka kere wadannan da ikon Allah. Mudai ci gaba da addu’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...