Daga Rahama Umar Kwaru
Kungiyar hadin kan ma’aikata ta kasa (JNPSNC) ta karrama gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf da babbar lambar yabo saboda jajircewarsa wajen kyautata jin dadin ma’aikatan gwamnati ta hanyar cika alkawarin mafi karancin albashi.
Shugaban ma’aikatan jihar Kano Abdullahi Musa ne ya bayar da kyautar a madadin kungiyar JNPSNC a wani bikin da aka gudanar a ranar Litinin.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.
Da yake jawabi a madadin majalisar, Abdullahi Musa ya yabawa irin nagartaccen jagoranci da gwamna Yusuf ke yi, inda ya bayyana shi a matsayin gwamna mafi jajircewa wajen kyautata jin dadin ma’aikata duk da kalubalen da ake fuskanta na tattalin arziki.
“Wannan karramawar wata shaida ce da ke nuna kyakkyawan shugabanci na gwamna da kuma jajircewarsa wajen ganin ma’aikatan gwamnati sun sami walwala yadda ya kamata,” inji shi.
RUMFOBA 94 ta Karrama Doguwa bisa gudunmawar ciyar da ilimi gaba da ya yi a Kano
A jawabinsa na godiya, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna jin dadinsa da karramawar tare da jaddada aniyar gwamnatinsa na samar da kyakykyawan yanayin aiki mai kyau ga ma’aikata.
Ya bayyana fara biyan mafi karancin albashin ma’aikata a matsayin wani tubali na ganin jihar Kano ta samu ci gaba mai inganci.
“Wannan karramawa ba ta ni kadai ba ce, har ma ga daukacin ma’aikatan Jihar Kano, wadanda jajircewarsu da kwazon su ne ke kawo nasarar da gwamnatinmu ke samu. Za mu ci gaba da ba da fifiko ga jin dadin su,” in ji Gwamna Yusuf.
Gwamnan ya kuma bukaci sauran jihohin da har yanzu ba su aiwatar da Karin mafi karancin albashin ga ma’aikatansu ba da su yi koyi da shi, yana mai jaddada cewa kyautata wa ma’aikata na da matukar muhimmanci wajen samun ci gaba mai dorewa da kuma kara samar da ayyukan yi.
Wannan karramawar ta kara tabbatar da martabar Gwamna Yusuf a matsayin shugaba mai hangen nesa mai himma wajen ciyar da jihar Kano gaba da kuma inganta rayuwar al’ummarta.