Hedikwatar tsaron Nijeriya ta bayyana cikakken ‘yan bindigar nan mai suna Bello Turji, a matsayin gawa ne ke tafiya.
Wannan dai ya biyo bayan barazanar da dan bindigan ya yi kan sojoji da al’ummomin a jihar Zamfara.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa a cikin wani sabon faifan bidiyo da Bello Turji ya saki anji ya na kalubalantar sojojin Nijeriya, inda ya zarge su da kai wa tsofaffi hari tare tare da neman a sako wani abokinsa mai suna Baka Wurgi da hukuma ke tsare da shi.
Mafi Karancin Albashi: JNPSNC ta baiwa Gwamnan Kano lambar yabo
Ya kuma yi barazanar kai hari a sabuwar shekara mai kamawa ta 2025 matukar ba a biya masa bukatunsa ba.