Dan jihar Kano ya zama zakara a gasar musabakar al’qur’ani ta Kasa

Date:

Daga Umar Sani Kofar Na’isa

 

Wani dalibi dan jihar Kano mai suna Bukhari Sunusi Idris ya zama zakara a gasar karatun alkur’ani ta kasa karo na 39.

A ɓangaren mata kuma Gwana Rumaisa Tahir Daga jihar Gombe ce ta zamo zakariyar gwajin dafi kuma ita ce gwarzuwar bana 39th.

Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci ta Jami’ar Usman Danfodio dake Sokoto ita ce ta shirya musabakar a jihar Kebbi .

Kwamitin amintattu na malamai karkashin jagoranci Farfesa Sa’adiya Omar OON da Mal. M.K. Jabo Mataimakin Shugaban, da sauran manyan malamai sune suka saka jagoranci tafiyar da musabukar.

Talla

Bukhari Sunusi ya fito ne daga karamar hukumar Gezawa .Ya kuma lashe gasar karatun Qur’ani ne Hizifi 60 da tafsiri .

Sakamakon musabukar ya kasancewar cewa Bukhari Sunusi daga Kano Wanda ya zamo na daya ya samu maki 98.20

Sai Nuhu Muhammad daga Gombe da ya zama na biyu da maki 96.20

Sai Mustapha Muhammad da ya zama na uku daga Kebbi da maki 95.30

Sai Kuma Nafiu Ridwan Katsinawa daga Bauchi da ya zama na hudu da maki 93.40.

BUK Ta Daga Likkafar Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo zuwa Matsayin Farfesa

Yayin da Kuma Safiyanu Muhammad daga Kaduna da ya zama na biyar da maki 93.10

A wani karimci, Gidauniyar Ganduje foundation ta bayar da gudummawar Naira miliyan 2.25 ga wadanda suka yi nasara.

Gasar wacce aka gudanar a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Jihar Kebbi, masu shirya gasar sun yaba da yadda aka kammala cikin nasara.

A wajen gasar an baiwa Bukhari Sunusi kyautar mota da kudade masu yawa.

Mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na III da gwamnan Kebbi Nasiru Idiris da Ministan kasafin kudin Abubakar Bagudu da manayan yan siyasa suna daga cikin mahalarta taron rufe musabukar.

Anan gaba ake sa ran gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf zai karbi bakuncin gwarzon shekarar dan karramashi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin kisa a R/Zakara: Gwamnatin Kano za ta kafa kwamiti – Waiya

Gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta gudanar da...

Majalisar Dokokin Kano ta yi Doka kan masu tufar da yawu da majina a titi

Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da dokar cin...

Sanata Barau zai baiwa dalibai 1,000 tallafin karatu a Kano ta tsakiya da ta Kudu

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau...

Kamfanin Gerawa ya ba da tallafin Kwamfutoci 100 ga al’ummar Gezawa

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa   Kamfanin shinkafa na Gerawa Rice Mills...