Gwamnati Ta Tashi Kasuwar Kwanar Gafan dake Garun Malam a Kano

Date:

Daga Safiyanu Dantala Jobawa

 

Majalisar karamar hukumar Garun mallam a jihar Kano, ta baiwa mazauna kasuwar Kwanar Gafan wa’adin kwana bakwai da su tashi daga cikin kasuwar har zuwa wani lokaci nan gaba.

Shugaban karamar hukumar, Barr. Aminu Salisu Kadawa ne ya bada umarnin hakan a wajen bikin kaddamar da sake fasalin farfado da tattalin arzikin yankin.

Kadawa ya ce “Duba da yadda aka mai da kasuwar tamkar wata mafaka da cibiyar yada badala maimakon ainihin yin abun da yasa aka kafa kasuwar tun farko, amma Mun fahimci kasuwar ta sauka daga Kan Manufar da tasa aka samar da ita. Ya bukaci mazauna kasuwar da su tattara kayansu su bar wajen, tun kafin ranar 1 ga watan Janairu 2025, idan ba haka ba duk wanda aka kama za a hukunta shi.

Talla

” Nan gaba Kadan za mu bayyana lokacin da za a yi bikin sake bude kasuwar don cigaba da kasuwancin iri daban-daban ba ma na kayan Gona ba har nau’in sauran ababan more rayuwa don inganta tattalin arzikin yankin”. Barr Aminu Salisu

Ya bukaci yan kasuwa da zo domin saka jarinsu a kasuwar, domin za a gyara kasuwar ta yadda zata yi dai-dai da zamani.

Kwankwaso ya taya Ganduje Murnar Cika shekaru 75

Wani malamin addinin islama, Imam Abdullahi Yusif Chiromawa, ya bayyana cewa kasuwar Kwanar Gafan ta zama barazana ga tarbiyar yaransu, ya ce abubunwan da Ake a kasuwar ya sabawa shari’ar musulunci.

Malam Abdullah ya ce Kasuwar ta zama wajen aikata zinace-zinace ,Luwadi, da madigo ga matasa da kuma kawo matan aure, Sannan kuma mafaka ce ga Barayi da yan fashi da masu safarar mugagga kwayoyi, don haka ya gode shugaban karamar hukumar bisa namijin kokarin da ya nuna don kaucewa kara fadawa cikin fushi Allah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...