EFCC ta gurfanar da wanda ake da zargi da almundahanar taki a Kano

Date:

Hukumar EFCC ta gabatar da wani mutum mai suna Sanusi Hashim bisa zargin almundahanar taki ta naira miliyan 108.

An gabatar da Hashim ne a babbar kotun tarayya da ke Zaria a gaban Mai shari’a Kabiru Dabo kan zargin rashawa, wanda ya saɓa da sashe na 293, wanda kuma ya cancani hukunci a ƙarƙashin sashe 294 na kundin laifuka.

Talla

An zarge shi ne da karɓar naira miliyan 108 daga Ahmad Mohammad Liman da Bashiru Mohammad domin ya kawo musu taki, amma ya ƙi kai musu, zargin da ya ƙaryata.

A ƙarshe Mai shari’a Dabo ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 10 ga Fabrairun 2025, sannan ya buƙaci a ajiye wanda ake ƙara a kurkuku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...