Ya kamata Gwamnatin tarayya ta da tallafi a Hajjin 2025 – Hukumar Jin dadin alhazan Kano

Date:

Darakta-Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya yi kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya da ta duba yiwuwar ba da tallafin aikin hajjin 2025.

Danbappa ya yi wannan roko ne a wata hirar kai tsaye a shirin Barka da Hatsi na gidan rediyon Freedom da safiyar yau.

Talla

Alhaji Lamin Rabi’u ya bayyana cewa kalubalen da ake fama da shi a fannin tattalin arziki a kasar nan ya yi matukar tasiri ga rayuwar ‘yan kasa da dama, wanda hakan ya sa masu niyyar zuwa aikin Hajji ke shan wahala wajen biyan kudin aikin Hajji.

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun hutun kirsimeti da sabuwar shekara

Ya jaddada cewa bayar da tallafin zai saukakawa musulmai wajen samun damar biyan kuɗin sauke farali a bana.

“Bisa la’akari da halin da al’umma su ke ciki, ina kira ga Gwamnatin Tarayya da ta duba yiwuwar bayar da tallafi domin amfanin al’ummar Musulmi. Wannan zai sanya mutane da yawa su sami damar iya biyan kudaden aikin hajjin bana,” in ji shi.

Bugu da kari, Alhaji Lamin Rabi’u ya shawarci dukkan maniyyatan da ke da sha’awar halartar aikin hajjin 2025 da su tabbatar sun biya kudaden ajiya ta hanyar banki kafin cikar wa’adin da aka sanya.

Ya kuma jaddada mahimmancin biyan kudi da wuri domin saukaka tsare-tsare da dabaru na aikin hajji.

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta Dukufa wajen ganin an samu nasarar gudanar da aikin Hajjin bana cikin nasara ga dukkan maniyyatan jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...

Tinubu ka fadawa yan Nigeria Inda ka tsaya har kwana 5 bayan taron BRICS – ADC

    Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC ta soki Shugaban...

Da dumi-dumi: Yadda akai Jami’an tsaro suka kama ni -Danbello

Rahotannin sun tabbatar da cewa jami'an tsaro a Nigeria...