Tinubu ya gargaɗi ƴan siyasar dake alakanta mace-mace a wurin rabon abinci da salon mulkinsa

Date:

Ministan yada labarai da wayar da kan al’umma, Mohammed Idris, ya gargadi ƴan siyasa kan alakanta mace-macen da suka faru a lokacin rabon abinci a Oyo, Anambra da Abuja da sake fasalin tattalin arzikin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sai dai ya jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan lamari da ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 70, ciki har da yara kusan 40.

Talla

Daily Trust ta rawaito cewa ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi, ya dora alhakin mace-macen a kan gazawar tsarin da Najeriya ke yi a halin yanzu a kasar.

Ministan a cikin wata sanarwa da ya fitar mai dauke da sa hannun babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Rabiu Ibrahim, ya ce bala’o’in sun nuna muhimmancin tabbatar da yadda jama’a ke gudanar da irin wadannan ayyukan na agaji, musamman a lokutan bukukuwa.

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun hutun kirsimeti da sabuwar shekara

Ya amince da kyakkyawar niyya na masu shirya taron na neman kawo dauki ga marasa galihu a cikin al’umma, inda ya kuma gargadi duk daidaikun mutane da kungiyoyi masu shirya irin wannan lamari da su bi umarnin babban sufeton ‘yan sanda, Mista Kayode Egbetokun domin kula da jama’a kan matakan tsaro.

Ya kuma jaddada cewa, hadin gwiwa da ‘yan sanda da hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) na da matukar muhimmanci wajen kare rayuka da kuma tabbatar da cewa irin wannan kokari na taimakon mabukata ba zai haifar da da mai ido ba.

A karshe ya gargaɗi ƴan siyasa, musamman na bangaren adawa da su guji irin waɗannan kalamai, inda ya ce hakan rashin adalci ne tsantsa.

Ya kara da cewa sauye-sauye na tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ke yi ya fara haifar da ɗa mai ido a kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...