Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Kamfanin man NNPCL a Nijeriya ya zaftare farashin litar fetur zuwa N899 irin na Dangote.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar PETROAN Joseph Obele ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema a ranar asabar.
Sanarwar ta ce sashin Kasuwanci na NNPC ta fitar da sabon farashin man kamar haka: Lagos, N899.0; Warri, N970.0; Oghara, N970.0; Port Harcourt, N970.0. sai kuma Calabar, N970.0.

Kamfanin NNPLC ya yi wannan ragi ne bayan da matatar mai ta Ɗangote ta fitar da sanarwar rage farashin man.
Da yake tsokaci kan rage farashin man Shugaban kungiyar PETROAN Billy Gillis Hary ya ce rage farashin man zai samar da sauki ga masu ababen hawa musamman a wannan lokaci na bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara.
Fulawa Da Dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa Za Su Ci N125m A 2025
” Muna yaba wa Kamfanin NNPLC bisa rage yawan kudin litar mai, wanda hakan ya nuna kwazon kamfanin na samar da sauki ga yan Nigeria”.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a ranar 19 ga watan Disamba, 2024, kamfanin NNPLC ya rage farashin man kafin wannan lokaci.