Wata babbar kotun jihar Kano a ranar Larabar da ta gabata ta umurci gwamnatin jihar Kano da ta biya naira biliyan takwas da dubu dari biyar da goma sha daya (N8, 511, 000, 000:00) ga Kamfanin Lamash Properties Limited wadanda su ka yi Gine-gine a tsohuwar Daula Otel da gwamnan jihar, Abba Kabir ya rushe.
Kotun ta kuma umarci wadanda ake kara da suka hada da gwamnatin jihar Kano, Gwamna Abba Kabir da kuma babban lauyan jihar su biya karin naira miliyan goma (N10, 000, 000.00) a matsayin kudin shigar da karar.
Gine-ginen, wadanda aka rushe bisa umarnin gwamna a watan Yuni, 2023, akan su ne kamfanin Lamash Properties suka shigar da karar, inda suka yi ikirarin cewa barnar da gwamnan ya yi bai dace ba.

An shigar da karar ne gaban wata babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin mai shari’a Sunusi Ma’aji, masu shigar da karar sun ce sun sami damar fara gine-gine a filin na Daula Otel ne bisa ka’ida ta hanyar kulla yarjejeniya da gwamnatin jihar a karkashin gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje.
Lamari Mai dadi: Ɗangote ya rage farashin man fetur
Kamfani Lamash, ta bakin lauyansa, Nureini Jimoh, SAN, ya ce yarjejeniyar da aka rattabawa hannu da gwamnatin jihar Kano domin bunkasa wurin domin samun riba, ba ta kare ba, amm Gwamna Yusuf ya yanke shawarar rusa wurin.
Lauyoyin Wadanda ake karar da suka hadar da Ibrahim Wangida da Bashir Muhammad, sun shigar da takardar sheda kan lamarin kamar yadda kotun ta bayyana.
A yayin da yake yanke hukuncin a ranar Laraba, Mai shari’a Ma’aji ya amince da cewa an rusa gine-gine ba bisa ka’ida ba don haka ya ce tun da ba za’a iya dawo da ginin ba, to ya zama wajibi wadanda ake kara su biya kuɗin da aka kashe wajen ginin.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a watan Satumba, 2023, wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano, ta yanke Hukuncin cewa gwamantin Kano ba ta rushe shagunan dake masallacin idi na Kofar Mata akan ka’ida ba, don haka ta umarci gwamnati ta biya diyya ta Naira biliyan 30 .
Idan mai karatu bai manta ba a ranar Asabar, 3 ga watan Yuni, 2023, kwanaki kadan bayan rantsar da shi, Gwamna Yusuf da kan sa ya jagoranci tawagar ruguza gine-ginen da ya yi imanin an gina su ba bisa ka’ida ba a filayen gwamnati.