Kungiyar DOOGA ta Samar da Cibiyar koyar da sana’o’i a makarantar yan mata ta Dala

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Kungiyar tsofaffin daliban makarantar yan mata ta Dala (Dooga) ta gina sakatariyarta tare kuma da samar da cibiyar koyar da sana’o’i ga daliban makarantar duk a cikin shekara guda.

“Muna cikin farin ciki kasancewar an tara musu kudi da adadinsu ya kai Naira miliyan dari da sittin tun a watan Afirilu na shekarar bara 2023, Wanda da shi ne mu ka samar da Sakatariyar Kungiyar mai suna Rabi Tajudeen Dantata Skills Aquasition center & Dooga Secretariat mai dauke da Gini hawa daya”.

Talla

Shugabar kungiyar ta kasa Hon. Hajiya Saudatu Sani ce ta Bayyana haka yayin taron manema labarai a yau Alhamis.

A kasan Sakatariyar Akwai Babban dakin taro da ofisoshi gudanar da sha’anin Kungiyar, yayin da saman kuma ya kasance cibiyar koyar da sana’o’i ga dalibai mai dauke da ajin koyon dinki wanda aka sanya masa kekuna dinki guda 30, sai dakin gwaji da kuma madafa.

Rushe Daula Otel: Kotu Ta Ci Tarar Gwamnatin Kano

“Fannin gyara mun sabunta tsaffin Ajujuwa 44 tare da Samar da kujerun zama Dubu bakwai 7000, da Samar da ruwan sha in da suka gina tuka tuka 100, ba shakka sai dai ace makarantar Yan mata ta Dala ta zama zakaran gwajin dafi”. A cewar Shugabar Kungiyar Dooga.

Haka Kazalika, ta koka kan yadda wasu Malamai mazauna gidajen kwatas din makarantar da su ka yi ritaya suka ki tashi daga gidajen, sannan kuma basa gyara sai kiwo wanda ke bata wuri, da kuma amfani da rufin kwano wanda zai iya illata dalibai, don haka tace tana Kira ga gwamnatin jihar Kano ta dauki matakin da ya dace, don kuwa akwai malaman makarantar masu himma daya kamata ace su ke cikin gidajen.

Daga karshe ta yi kira ga yan Siyasa da Mukarraban Gwamnati da su kasance masu bibiya sannan kuma su tabbatar sun dinga sauke nauyin kasafin kudin duk da suka rubuta da hannun su, don kuwa su ma bibiya ne yasa suka cimma burinsu da kuma sauke nauyin kudin da al’umma su ka tara musu har Naira miliyan dari da sittin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...