Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Matatar mai ta Dangote ta rage farashin man fetur zuwa N899.50k kan kowace lita.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban sashin hulda da jama’a na kamfanin Anthony Chiejina ya fitar a safiyar ranar Alhamis.

Kamfanin ya ce an dauki matakin ne domin “samar da saukin da yan Najeriya ke bukata a wannan lokaci.
Yanzu-yanzu: Tinubu ya sake baiwa Musa Iliyasu Kwankwaso Mukami
Matatar mai ta farko mai zaman kanta a Afirka, wacce a baya ta rage farashin zuwa N970 ga kowace lita a ranar 24 ga watan Nuwamba, yanzu ta sanar da sabon farashin N899.50 kan kowace lita. Wannan ragi an yi shi ne don saukaka farashin sufuri ga yan Nigeria a lokacin bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara,” in ji sanarwar Anthony Chiejina.
Ya kara da cewa kamfanin ya kuma samar da wata garabasa a wannan lokaci duk dai domin saukakawa al’umma su sami damar gudanar da Zirga-zirga cikin sauki.
Kamfanin ya kuma godewa al’ummar Nigeriya bisa goyon bayan da suke ba su a ko wanne lokaci.