Gwamna Kano ya kara mutum 1 cikin kwamishinonin da Majalisa ta tantance

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

Majalisar dokokin jihar Kano,ta tabbatar da sunayen mutane bakwai da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin tantance don ya nada su a matsayin kwamishinoni kuma mambobin majalisar zartarwa ta jihar.

Kafin tabbatar da su, sai da mutanen bakwai suka kwace sama da sa’o’i uku da rabi, inda majalisar ta amincewa gwamnan ya nada su a matsayin kwamishinoni.

Talla

Kakakin majalisar Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore, ya bayyana cewa gwamnan ya sake aiko da Sunan Nura Iro Ma’aji domin tantance shi a matsayin kwamishina bayan wadancan sunaye na Mutane shida da aka fara tura sunayensu.

Ga sunayen wadanda Majalisar ta Amince da su:

Tsohon shugaban ma’aikata: Shehu Wada Sagaji, wanda aka sauke shi daga mukaminsa a ranar Alhamis din da ta gabata.

Kotun Ƙoli ta kori ƙarar da ke neman ta sauke Tinubu daga shuagaban Nigeria

1. Ambassador Ibrahim Waiya

2. Shehu Wada Sagagi

3. Abdulkadir Abdulsalam

4. Gaddafi Sani Shehu

5. Dr. Dahiru Hashim Muhammad

6. Dr. Ismail Aliyu Dannaraya

7. Nura Iro Ma’aji

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...