Daga Isa Ahmad Getso
Sabon kwamishinan Ilimi na jihar kano Dr. Ali Haruna Makoda ya kama aiki a hukumance, inda ya yi alkawarin kara bullo da wasu shirye-shirye da nufin bunkasa fannin ilimi a jihar.
Da yake jawabi ga ma’aikata, yan uwa da abokan arzikin da suka yi masa rakiya, Dr. Makoda ya amince da dimbin tsare-tsare da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta bullo da su tare da bayyana aniyarsa ta ciyar da su gaba.
Ya kuma jaddada bukatar yin aiki tukuru da jajircewa domin ganin ma’aikatar ta samu ci gaba.

Sabon Kwamishinan ya baiwa ma’aikatan tabbacin ci gaba da fadada shirye-shirye masu kyau da tsohon kwamishinan ma’aikatar ya bullo da su.
Dr. Ali Makoda ya bukaci ma’aikatan da su kasance masu ba da gudunmawa wajen aiwatar da manufofi da tsare-tsare da gwamnati mai ci ta bullo da su domin amfanin jama’a da jihar.
Gwamna Kano ya kara mutum 1 cikin kwamishinonin da Majalisa ta tantance
Kwamishina mai barin gado Alhaji Umar Haruna Doguwa ya nuna jin dadinsa da samun damar yin aiki a ma’aikatar tare da bayyana wasu nasarorin da aka samu a zamaninsa.
Nasarorin sun haɗa da: Ƙara yawan kasafin kuɗin da ake warewa fannin ilimi, Inda aka ware 30% a cikin 100 a Shekarar 2024 da 31% a Shekarar 2025.
“Gwamnatin gyaran makarantu a fadin kananan hukumomi 44
– Gina ajujuwa da ƙera kayan ɗalibi mai kujeru 3.
“Samar da kayan aiki a makarantu da inganta tsarin ciyarwa a makarantu
Babban sakataren ma’aikatar ilimi, Alhaji Bashir Baffa Muhammad, ya yi addu’ar Allah ya baiwa kwamishinonin biyu ikon yi musu jagoranci a sabbin ayyukan da aka ba su.