Hukumar KNUPDA ta Bayyana Ainahin Abu da zata Yi a Filin Shahuci

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Hukumar tsara burane ta jihar kano KNUPDA ta musanta labarin da ake yadawa cewa tana kokarin yanka shaguna a filin Shahuci dake karamar hukumar Birni.

“Ba shaguna mu ke ginawa a shahuci ba, muna yin irin yan shagunan nan ne na wucin gadi, kuma muna yin hakan ne domin amfani masu Kasuwanci a wurin tare da tsaftace birnin Kano kamar yadda dokar ta dorawa hukumarmu wannan aikin”.

Shugaban hukumar Arc. Ibrahim Yakubu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta hukumar KNUPDA Bahijja Malam Kabara ta aikowa kadaura24.

Talla

Sanarwar ta ce wasu marasa kishin jihar kano ne suke ta yada cewa gwamantin Kano ta na son yanka shagunan saboda su bata sunan gwamantin, ” to muna sanar da su cewa abun da suka yi ya sabawa ka’idar Addinin Musulunci domin musu sun sanya firgici a zukatan masu Sana’a a wurin kuma haramin ne firgita Musulmi”.

Arc. Ibrahim Yakubu ya kara da cewa gwamantin jihar kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ba ta da wani kudiri na raba wani ko wasu da sana’o’insu, amma hakan ba zai hana yin tsare-tsaren da zasu Inganta jihar kano ba.

Yanzu-yanzu: Gwamnan Kano ya aike da suneyen wadanda zai nada Kwamishinoni ga Majalisar jihar

Yace yana kira ga al’ummar jihar Kano da su yi watsi da wancan labarin domin bashi da tushe ballantana makama, kawai gwamnati zata cigaba da bujiro da tsare-tsaren da zasu ciyar da gidan nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...