Yadda Mai aikin shara a Kano ya Mayar da Naira Miliyan 40 da ya tsinta

Date:

Wani mai aikin sharar asibiti a Kano ya mayar da kudin da ya tsinta kimanin Naira miliya 40 ga mai su.

Malam Aminu Umar Kokar Mazugal ya tsinci kudin ne a dalolin Amurka a cikin wata jaka da mai su ya manta a Asibitin Abubakar Imam da ke unguwar Fagge.

Talla

Malam Aminu wanda matsakaicin ma’aikaci ne ya tsinci kudin a cikin wata jaka kuma ya mayar da kudin ga mai su, Alhaji Ahmed Abubakar, wanda ya manta da su a lokacin da ya je dubiyar mara lafiya a asibitin.

Alhaji Ahmed ya manta da kudin ne a wurin da ya dan zauna na dan lokaci a wurin ajiye motoci da ke kusa da masallaci, inda daga bisani ya wuce domin shiga jirgin sama.

Gwamnatin Kano ba zata saurarawa masu sayar da filaye ba bisa ka’ida ba – Kwamitin karta kwana

Malam Aminu ya shaida wa wakilin Daily trust cewa jim kadan da tafiyarsa mutumin ne shi kuma ya tsinci kudin a lokacin da yake aikin shara.

Ya ce daga bisani, bayan kimanin awa guda, mai kudin ya dawo yana cigiya, shi kuma ya mayar masa da kayansa.

Ya ce mai kudin ya yi masa kyauta amma ya ki amsa, duk da cewa ya ba shi lambar wayarsa, kuma mutumin ya yi alkawarin tuntubar sa idan ya dawo daga kasar waje.

Shugaban Asibitin, Dokta Aminu Imam Yola, ya tabbatar da faruwar lamarin yana mai cewa hukumar gudanarwar asibitin ta sanar da Ma’aikatar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano domin a karrama Malam Aminu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...