Sarki Sanusi II ya Magantu Kan Hana shi zuwa Bichi da jami’an tsaro suka yi

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ce har yanzu masarautar Kano ba ta da masaniya kan dalilan da suka sanya jami’an tsaro suka yiwa masarautar kawanya tare da hana shi zuwa Bichi a makon jiya.

Kadaura24 ta ruwaito cewa jami’an ‘yan sanda da jami’an DSS sun tare hanyar shiga fadar Gidan Rumfa, inda suka hana shiga da fita a ranar juma’ar data gabata.

Ko da yake ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro ba su bayyana dalilin daukar matakin ba, amma majiyoyi sun ce hakan ba zai rasa nasaba da nadin sabon Hakimin Bichi, Munir Sanusi, wanda sarkin ya shirya yi masa rakiya a ranar.

Tuni dai gwamnatin jihar Kano ta fusata kan lamarin, inda ta zargi gwamnatin tarayya da alhakin daukar tura jami’an tsaron domin kaiwa sarkin cikas.

Talla

Sarkin a ranar Larabar nan, yayin da ya karbi tawagar Dagatai da masu unguwanni Bichi da suka zo yi masa godiya bisa nada musu Hakimin da aka yi, Inda ya fada musu cewa har yanzu ba a samu cikakken bayani kan dalilin da ya sa aka rufe fadarsa ba a ranar da aka shirya kai musu hakimin.

“Wannan abu da ya faru, an yi shi ne kawai don daga hankali, kuma har yanzu ba mu san dalilin da ya sa hakan ta faru ba kuma wadanda ke da hannu ba su bayyana dalilin da ya sa suka aikata hakan ba. Duk da haka, wannan ba zai hana mu komai ba”. Inji Sarki Sanusi II

Kungiyar DHS International ta yi Aikin Dubawa da Rabawa Marasa Lafiya Magani Kyauta a Kano

“Ina mai tabbatar muku da cewa za’a saka wata ranar kuma za’a kawo muku Hakimin ku kuma komai zai gudana cikin kwanciyar hankali.”

Sai dai ya yi kira ga al’ummar Bichi da su kwantar da hankula su ci gaba da zaman lafiya kamar yadda aka san su da shi.

“Ku je ku sanar da jama’a su ci gaba da zaman lafiya da juna Sannan su yi addu’a. Koma dai halin da ake ciki, tabbas zaman lafiya da addu’a za su kawo ƙarshen sa.

A duk lokacin da ka ga mutum yana kokarin kawo cikas ga zaman lafiya da jama’a ke samu, to kar ka biye masa ,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa Bichi a wajensa gida ce, saboda a can ya rika zuwa yana yin hutunsa tun yana yaro har ya girma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...