Karamar hukumar Garun Mallam za ta rabawa Yan Firamare litattafai dubu 100

Date:

Daga Safiyanu Dantala Jobawa

 

Majalisar karamar hukumar Garun Malam ta yi alkawarin rab littattafai kimanin guda dubu dari daya (100.000) domin cigaban harkokin Ilimi a yankin.

Kadaura24 ta rawaito Shugaban karamar hukumar, Barista Aminu Salisu Kadawa, ne ya bayyana hakan a bikin mika tallafi wanda ya gudana a sakariyar karamar hukumar.

“Wannan na matsayin kason farko a jaddawalin tsarin bunkasa sha’anin ilimi da muka yiwa wannan karamar hukumar, kuma za mu cigaba da bullo da hanyoyin da zamu taimaka wa iyaye tare da daibai duba da irin yanayin da ake ciki na matsari rayuwa”. Inji Barr. Aminu Kadawa.

Talla

Ya sha alwashin ganin duk makarantar da ta yi fice a gasar da za a bijiro da ta nan gaba kadan an tallafa mata, kana ya roki malamai da su kara jajicewa akan aikinsu ba tare da kawo wani nakasu ba.

Tun da fari, sakataren ilimi na yankin Alh. Sabo Muhammad Chiromawa ya bayyana wannan tamkar wata yar manuniya ce da ke nuna gwamnatin jihar Kano karkashi Gwamna Engr Abba Kabir Yusif ta dawo da ruhin ilimin firamare wanda ya fada wani irin hali a baya.

Sarki Sanusi II ya Magantu Kan Hana shi zuwa Bichi da jami’an tsaro suka yi

Ya gode wa shugaban karamar hukumar Barista Aminu S Kadawa, bisa irin hangen nesan shi akan damuwa da ilimi yaran yankin.

Da ya ke mika sakonsa shugaban hukumar ilimin Bai-Daya(SUBEB) ta jihar Kano Malam Kabir Yusuf wanda ya samu wakilcin sakatariya a hukumar Hajiya Amina Umar, ya ce “Garun mallam ita ce ta farko wajen nuna damuwarta kan sha’anin ilimin al’ummarta. Kana ya ce duk bukatar da ake da ita, ma’aikatarsu a shirye ta ke.

Hajiya Amina ta mika tallafin littattafan ga wakilan makarantun faramare dana kananan makarantun sakandire da ke yankin.

Daga cikin mahalarta bikin, sun hadar da daraktan wayar da kai na SUBEB Balarabe Danlami Jazuli da Hajiya Maryam Hodi sai kuma Rano Zonal Alh Sunusi Uba Ahmad da sauran al’umma da ke yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...