Majalisar Dokokin jihar Adamawa ta amince da dokar kafa sabbin masarautu

Date:

 

Majalisar Dokokin jihar Adamawa ta amince da kudirin doka na kafa sabbin masarautu tare da nade sarakuna masu darajar ta daya a jihar.

Sabuwar dokar masarautun, wadda ke jiran amincewar Gwamna Ahmadu Fintiri, ta samu amincewa ne kwana kalilan bayan gwamnan ya rattaba hannu kan wata doka, Dokar Kirkiro Gundumomi ta Jihar Adamawa 2024, wadda ta samar da sabbin gundumomi guda 83 a ranar 4 ga Disamba.

Talla

A wata wasika da Mr. Fintiri ya aikewa ‘yan majalisar a ranar Litinin, ya bukaci su amince da kudirin doka da zai bayar da damar nade sarakuna da cire su daga mukamansu a jihar Adamawa.

Kudirin ya bai wa gwamnan ikon kafa karin masarautu tare da nada ko tsige shugabannin gargajiya.

Kungiyar DHS International ta yi Aikin Dubawa da Rabawa Marasa Lafiya Magani Kyauta a Kano

Kudirin dokar ya tsallake karatun farko da na biyu a Majalisar Dokokin Jihar a ranar Litinin.

Dokar ta rage tasirin Lamidon Adamawa, Alhaji Muhammadu Barkindo, ta hanyar takaita yawan kananan hukumomin da ke karkashinsa daga takwas zuwa uku.

Daily Nigerian

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...