Za a fuskanci hazo tsawon kwana uku a sassan Najeriya – NiMet

Date:

Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya, NIMET, ta yi hasashen cewa za a fuskanci yanayin hazo da kura a sassan Najeriya daga yau Litinin zuwa Laraba.

Hukumar ta ce yankunan Arewacin dama na tsakiyar Najeriya ne za su fi fuskantar yanayin na hazo da da kura.

Talla

NIMET, ta ce za a samu matsala wajen hangen nesa saboda hazon a tsawon kwanakin ukun.

Za mu biya kudaden daliban Kano da Ganduje ya gaza biyawa kudin makaranta a Cyprus – Gwamna Abba

Daga nan hukumar ta bukaci jama’ar da ke zaune a yankunan da hazon zai fi tsanani da su dauki matakan kariya musamman wadanda ke fama da wata lalura data shafi rashin kura ko hazo kamar Asma ko kuma cutukan da suka shafi numfashi.

Kazlaika NIMET, ya shawarci kamfanonin jiragen sama da ke zirga-zirga a Najeriya da su tabbata sun samu cikakken rahoton game da yanayin da za a iya kasancewa da shi a iya kwanakin da aka hasashen fuskantar hazo da kurar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...