Daga Sani Idris Maiwaya
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da kyautata rayuwar daliban Kano da ke karatu a kasar Indiya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24 a ranar Alhamis.
A ziyarar da Gwamna Yusuf ya kai ofishin jakadancin Najeriya dake birnin New Delhi na ƙasar India, ya tattauna da jami’an ofishin Jakadancin da nufin inganta alakar dake tsakanin kasashen biyu da tabbatar da tsaro, walwala, da nasarar karatun daliban Kano a Indiya.

Gwamnan ya jaddada muhimmancin tallafawa dalibai a kasashen waje, inda ya ce nasarorin da daliban suka samu a karatunsu ya na da matukar muhimmanci ga ci gaban Kano.
Ya kuma jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da kyawawan yanayin da dalibai za su yi karatunsu cikin nasara har su dawo gida don bayar da gudunmawa mai ma’ana ga ci gaban jihar.
Gwamnan Yusuf ya yaba da kwazon daliban Kano da ya tura India domin yo karatun digiri
A nasa jawabin, mukaddashin shugaban Ofishin Jakadancin Najeriya a birnin New Delhi, Ubong Akpan Johnny, ya yabawa gwamnan bisa kokarin da yake yi tare da tabbacin ofishin jakadancin zai ba shi cikakken hadin kai.
Johnny ya jaddada aniyar ofishin jakadanci na ba da fifiko ga walwala da lafiyar daliban Kano, da ma sauran al’ummar Nijeriya mazauna Indiya.