Babbar kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta, a Shahuci Kano, ta dage sauraren da’awar shari’ar da iyayen yara da malaman Makarantar Imam Malik Bin Anas Littahafizul Qur’an wattarbiyya Wat Ta’alim, dake unguwar Sabuwar Gandu a karamar hukumar Kumbotso, kan karar da suka shigar da wasu mutane 8 , bisa zargin siyar da filin da tsohon sanatan Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayar a matsayin wakafi don gina makarantar isilamiya.
A zaman kotun na ranar Talata, lauyan masu kara barista Ahamed Makari, ya roki kotun ta ba su damar sanya sunan tsohon Sanatan Kano ta tsakiya, Mallam Ibrahim Shekarau , da kuma wadanda suka zama wajibi a sanya su, a kunshin shari’ar dan sadasu da sammaci a gajeren lokaci don su gabatar da da’awarsu.

Luyan da ke tsayawa wadanda aka karar, Barista Shehu Mai-Yaki, bai yi suka ba, kan rokon lauyan masu karar.
Alkalin kotun mai shari’a Mallam Muhammad Sani Ibrahim, ya amince da rokon.
Iyayen yaran da malamansu, sun cika harabar kotun don ganin yadda zata kasance a matsayinsu na masu kara.
A bangaren lauyan wadanda aka yi kara Barista Shehu Mai-yaki, ya ce ba zai yi magana da manema labarai ba har sai ya nemi izini daga na sama dashi.